Hukumar kula da shige da fice ta kammala shirin daukan matasan Najeriya aiki

Hukumar kula da shige da fice ta kammala shirin daukan matasan Najeriya aiki

Kwamitin gudanarwa dake kula da hukumar tsaro ta farin kaya, Civil Defence, hukumar kashe gobara, Fire Service da hukumar kula da shige da fice, Immigration, watau CDFIB, ta amince da bukatar hukumar kula da shige da fice na daukan sabbin ma’aikata a shekarar 2020.

Jami’i magana da yawun hukumar kula da shige da fice ta Najeriya, NIS, Sundaye James ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a, inda yace kwamitin gudanarwa a karkashin jagorancin Ministan cikin gida Rauf Aregbesola ne ta amince da daukan aikin.

KU KARANTA: Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari

Hukumar kula da shige da fice ta kammala shirin daukan matasan Najeriya aiki
Hukumar kula da shige da fice ta kammala shirin daukan matasan Najeriya aiki
Asali: UGC

“Za’a dauki makonni hudu ana hidimar daukan aikin daga ranar da aka sanar a hukumance, don haka ake kira ga jama’a su yi amfani da wannan dama domin su nemi aikin nan.” Inji shi.

Haka zalika Sunday ya gargadi jama’a daga shiga yanar gizon da ba na hukumar ba da nufin neman aikin, inda ya bayyana sahihin adireshin yanar gizon hukumar kamar haka www.nisrecruitment.org.ng.

“Don haka hukumar take kara kira ga jama’a su tabbatar da bin dokokokin hukumar wajen neman guraben ayyukan, kuma su sani cewa neman gurbin aiki a hukumar NIS kyauta ne, ba biya ake yi ba.” Inji shi.

A wani labarin kuma, rundunar Sojan saman Najeriya ta bankado wani sabon mafakar yayan kungiyar ta’addanci na Boko Haram a wani kauye dake Bula Korege inda suke sake tattaruwa a cikin dajin Sambisa, sai dai rundunar ta sake tarwatsa su.

Daraktan watsa labaru na rundunar, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, inda yace yan ta’addan na kokarin kai ma Sojoji da fararen hula hari ne a lokacin da rundunar Sojan saman ta bankado su.

Hakan yasa rundunar tura jiragenta na yaki domin tarwatsa yan ta’addan, inda suka yi musu ruwan bama-bamai inda suka kashe mayakan Boko Haram da dama tare da lalata mafakar tase tare da makamansu da sauran kayan aiki.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng