Fadar shugaban kasa tayi martani a kan 'harin' da aka kaiwa Buhari a Kebbi

Fadar shugaban kasa tayi martani a kan 'harin' da aka kaiwa Buhari a Kebbi

- Fadar shugaban kasa tayi martani a kan zargin kaiwa shugaban kasa Muhammad Buhari hari da aka yi a jihar Kebbi

- A wata takardar da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar, ya ce matashin dai masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne

- Kamar yadda fadar ta bayyana, masoyin shugaban kasar yayi yunkurin isa wajensa ne don su gaisa ba don cutarwa ba

Fadar shugaban kasa tayi martani a kan zargin kaiwa shugaban kasa Muhammad Buhari hari da aka yi a jihar Kebbi a ranar Alhamis.

Wani bidiyo dai ya bayyana inda wani matashi ke ta kokarin cafko shugaban kasa Muhammadu Buhari a bikin baje kolin kamun kifi da aka yi a jihar Kebbi. Wannan bidiyon kuwa ya jawo cece-kuce daga wajen ma'abota amfani da kafafen sada zumuntar zamani.

A wata takardar da mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar, ya ce matashin dai masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ba harar shi yayi niyya ba.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar Kebbi a ranar Alhamis don bude taron bikin baje kolin kamun kifi da al'adun gargajiya na jihar Kebbi.

Fadar shugaban kasa tayi martani a kan 'harin' da aka kaiwa Buhari a Kebbi
Fadar shugaban kasa tayi martani a kan 'harin' da aka kaiwa Buhari a Kebbi
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda wani matashi ya kaiwa Buhari damka a Kebbi (Bidiyo)

"Wannan ne karon farko da za a yi bikin wanda ke jawo hankulan jama'a daga kasashe daban-daban a shekaru 11 da suka gabata. An daina bikin ne tun bayan tsanantar rashin tsaro.

"A yayin da shugaban kasar ke rangadi a wajen don duba shinkafar da manoma suka kawo tare da daukar hoto dasu, sai wani matashi da farin ciki ya cika ya kusanto shugaban kasar. Yayi kokarin kaiwa garesa."

Ya kara da cewa, "Sanannen abu ne cewa hakan ba za ta yuwu ba. Jami'an tsaro kuwa sun hana matashi kaiwa gareshi wanda yasa matashin ya dinga kara yunkuri. A halin yanzu manyan 'yan adawa na cewa harar shugaban kasar yayi niyya. Makiya sun saba juya abun alheri zuwa sharri. Amma kansu suke ba haushi don kullum kasar na samu ci gaba,"

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel