Yajin aiki: An shiga gana wa tsakanin ASUU da FG

Yajin aiki: An shiga gana wa tsakanin ASUU da FG

An shiga wata gana wa tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar malaman jami'o'i (ASUU) a Abuja.

An shiga ganawar ne a ginin ma'aikatar kwadago da samar da aiyuka.

A yayin da minsitan kwadago da samar da aiyuka ke jagorantar bangaren gwamnatin tarayya, tawagar ASUU ta samu jagorancin shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi.

A ranar Litinin ne kungiyar ASUU ta sanar da fara yajin aikin jan kunne na makonni biyu a kan kin bayan malaman jami'a albashi saboda sun ki higa sabon tsarin biyan ma'aikatan tarayya albashi (IPPS) da gwamnatin shugaba Buhari ta kirkira.

Kazalika, ASUU tana son gwamnatin tarayya ta cika alkawuran da ta dauka a cikin yarjejeniyar da suka kulla yayin sulhunsu a shekarar 2009.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel