Halin da kadarorin Sanusi II da ke fadar Kano suke

Halin da kadarorin Sanusi II da ke fadar Kano suke

Falakin Kano mai murabus, Mujitaba Abubakar Abba, wanda shine tsohon babban sakataren fadar sarki Sanusi, ya bayyana halin da kadarorin sarkin suke ciki ga BBC.

Ya sanar da cewa dan uwansa ya bar daukacin dawakansa da kayan kawar daki da aka zuba a gidan sarkin domin amfanin wanda ya gajesa. Hakzalika an kwashe motocin da suke mallakin sarkin tare da killace su.

Tun daga dai ranar da aka tube masa rawaninsa ne aka fara kwashe kayansa, kuma an kammala ne a ranar Laraba kafin sarki Aminu Ado ya shiga gidan bayan sallar Magriba.

Duk wanda dai ya san tsohon Sarki Muhammadu sansui II, ya sansa da son kawa tun daga kan motocin alfarmarsa, dakin karatunsa da kuma manyan rigunansa.

Halin da kadarorin Sanusi II da ke fadar Kano suke
Halin da kadarorin Sanusi II da ke fadar Kano suke
Asali: Facebook

Falakin Kano mai murabus, Mujitaba Abubakar Abba, ya sanar da cewa mai martaba yafi damuwa da littatafnsa sama da komai bayan barinsa gidan sarautar.

Ya ce, “Ka san shi da harkar littatafai saboda haka su ne muka mayar da hankali wurin kwashewa domin killace su.”

DUBA WANNAN: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya zubar da hawaye yayin karbar takardar kama aiki

Ya kara da cewa Muhammadu Sanusi II ya so a bar su a masarautar idan har akwai tabbas cewa sabon sarkin zai yi amfani da su.

“A dakin karatun mai martabar, akwai littatafai a kalla 40,000 da doriya ban da kuma wadanda suke kan hanya daga Ingila zuwa Legas kusan 22,000 ne. A takaice dai darajarsu ba za ta rasa kai naira miliyan 200 ba banda wadanda ya mallaka tun yana makaranta.” Mujitaba yace.

Falaki Mujitaba ya ce ya tuna sa’ar da sarkin zai fice, ya ce duk wanda zai gajesa zai yi amfani da motocinsa, ba zai taba su ba.

Ya kara da bayyana cewa sun samu damar tattara kayan sakawar mai martabar. A cewarsa, “Sirdi daya ne kadai yace a daukar masa. Shi kuwa wannan sirdin na tarihi ne. Ya gajesa daga Ciroman Kano wato mahaifinsa, shi kuwa Ciroma ya gajesa ne daga Sarki Khalifa, Sarki Khalifa ya gajesa ne daga Sarki Abdullahi Bayero, shi kuma daga Sarki Abbas.”

Hakazalika, akwai takobinsa daya mai dumbin tarihi da ya bukaci a daukar masa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel