Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari

Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya halarci bikin al’adun gargajiya na kamun kifi da noma da aka gudanar a garin Argungu na jahar Kebbi karo na farko bayan kwashe tsawon shekaru 11 ba tare da an yi shi ba.

Mai magana da yawun shugaban kasa Buhari, Mista Femi Adesina ne ya bayyana haka inda yace shugaba Buhari ya bayyana dawowar bikin a matsayin wata manuniya dake nuni ga nasarar da gwamnatinsa ta samu wajen inganta tsaro a Najeriya.

KU KARANTA: Sanatoci sun sanya karatun digiri a matsayin karancin matakin neman mukamin shugaban kasa

Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari

Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari
Source: Facebook

Buhari ya nanata manufar gwamnatinsa na cigaba da inganta harkar tsaro domin habbaka bukukuwan al’adu da yawon bude ido, tare da janyo masu zuba hannu jari a bangaren nishadantarwa na Najeriya.

“Halartarmu yau a bikin baje kolin amfanin noma a garin Argungu tabbaci ne na manufarmu na inganta tsaro tare da fadada hanyoyin samar da abinci a cikin gida, muna sane da cewa an dakatar da wannan biki na shekara shekara tsawon shekaru 11 saboda matsalar tsaro.

“Amma cikin ikon Allah a yau bikin ya dawo, kuma ina fatan ya dawo da alheri, baya ga murnar dawowar wannan biki, muna farin cikin cigaba da aka samu a fannin samar da tsaro a yankin nan, ina kara sanar daku cewa an fara gasar tseren motoci daga Abuja zuwa Argungu a ranar Laraba.” Inji shi.

Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari

Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari
Source: Facebook

Haka zalika Buhari ya bayyana cewa akwai ire iren bukukuwan al’adu na Argungu da ake gudanarwa a duk fadin kasar nan, wanda ke kara dankon zumunci a tsakanin yan Najeriya tare da nuna ire iren al’adun dake kasar nan ga bakin kasashen waje.

“Wadannan bukukuwa suna samar da ayyukan yi ga yan Najeriya a bangaren yawon bude ido, wanda a yanzu haka mun tabbata da sauran aiki wajen inganta shi, don haka dole ne mu cigaba da taimakawa wajen kambama ire iren tarukan nan.

Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari

Dawowar bikin al’adun gargajiya na Argungun tabbaci ne na tsaro ya inganta – Buhari
Source: Facebook

“Ina amfani da wannan dama wajen yaba ma gwamnatin jahar Kebbi, mai martaba Sarkin Argungu, Ministan watsa labaru, gwamnan babban bankin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki wajen shirya taron a matakin karamar hukuma, jaha da gwamnatin tarayya.” Inji shi.

Shugaban kasa ya bayyana cewa a shekarar 2015 gwamnatinsa ta kaddamar da tsarin samar da abincin don ciyar da al’ummar kasa a jahar Kebbi, kuma duba da amfanin gona da aka bajekolinsu a taron ya nuna an samu nasara gagaruma ga tsarin siyar da kasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel