An maka gwamnatin Najeriya da jihar Kano gaban UN a kan tsare Sanusi II

An maka gwamnatin Najeriya da jihar Kano gaban UN a kan tsare Sanusi II

Kungiyar habaka tattalin arziki da kuma duba manyan ayyuka (SERAP) ta mika korafin gaggawa zuwa ga majalisar dinkin duniya a kan tsarewa tare da yadda ake kaskantar da tubabben sarkin Kano, Malam Muhammadu sansui II.

A koken mai kwanan wata 11 ga watan Maris din 2020 wanda mataimakin daraktan SERAP din, Kolawale Oluwadare yasa hannu, ya ce: “Tsare Sanusi Lamido da ake yi ya ci karo da yancinsa kuma babu wata hujja a shari’ance. Hakazalika, tsaresa da ake yi bai cika sharuddan da duniya ta tanadar ba."

“Kamawa da tsare tsohon sarkin babban lamari ne na take hakkinsa na dan Adam. Gwamnatin Najeriya da jihar kano sun take hakkinsa karkashin kundun tsarin mulki na 1999 da kuma dokar duniya,” ya ce.

SERAP ta maka gwamnatin Najeriya da jihar Kano gaban UN a kan tsare Sanusi II

SERAP ta maka gwamnatin Najeriya da jihar Kano gaban UN a kan tsare Sanusi II
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya zubar da hawaye yayin karbar takardar kama aiki

A wasikar da aka mika ga Jose Guevera Bermudez, shugaban kungiyar aiyukan, SERAP tayi kira ga kungiyar ayyukan a kan “Ta fara kokarin shiga cikin lamarin tsohon sarkin tare da turo wasikar gaggawa ga Najeriya da jihar Kano don jin dalilin kama shi, tsare shi da kuma kaskancin da yake fuskanta.”

SERAP ta kara da kira ga kungiyar ayyukan da ta mika bayanin da ke bayyana cewa an take hakkin sarkin tare da katsalandan ga kundun tsarin mulkin Najeriya. Ta bukaci kungiyar da tayi kira a kan a saki sarkin da gaggawa.

Kamar yadda SERAP ta bayyana, “Muna bukatar kungiyar ayyukan da ta umarci gwamnatin Najeriya da ta jihar Kano da ta bincika tare da damko duk masu hannu a kama shi, ci gaba da tsare shi da kuma kaskantar da shi.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel