Wata mata ta fashe da kuka bayan an yi mata kyautar N65,000, bayan shafe shekaru 8 tana talla ba ta tara komai ba

Wata mata ta fashe da kuka bayan an yi mata kyautar N65,000, bayan shafe shekaru 8 tana talla ba ta tara komai ba

- Wata tsohuwa 'yar kasar Ghana da take talla mai suna Diana Danso ta zubar da hawaye sosai bayan anyi mata kyautar naira dubu sittin da biyar

- Wannan kudi dai Ibrahim Oppong Kwarteng ne ya bata, wanda ya samar da gidauniyar Crime Check Foundation

- Matar ta bayyana cewa dan jarinta duka dubu goma sha uku ne, inda take amfani da shi wajen kula da kanta da kuma 'ya'yanta guda biyu

Diana Danso, wata mata 'yar kasar Ghana da take sana'a akan titi na tsawon shekaru 8, anyi mata kyautar ba zata ta naira dubu sittin da biyar (N65,000), inda hakan ya sanya ta zubar da hawaye.

Mutumin da yayi mata wannan kyauta ya wallafa hotonta a shafin gidauniyarsa na Facebook, inda ya bayyana matar idonta cike da kwalla.

Mutumin mai suna Ibrahim Oppong Kwarteng, wanda ya samar da gidauniyar ta Crime Check Foundation, shine ya bawa matar wannan kyauta, a matsayin sadaka da gidauniyar take yiwa mutane akan titi.

KU KARANTA: Dalibi ya mance takardunsa a gida, iyayensa sun dauko jirgin sama sun kawo masa takardun makaranta sun koma gida

Rahotanni sun nuna cewa matar mai matsakaicin shekaru tana dan sayar da kayanta da jari wanda bai wuce na naira dubu goma sha uku ba (N13,000), wanda hakan yayi kadan musamman idan aka yi la'akari da yanayin tattalin arzikin kasar ta Ghana.

A cewar Diana Danso, da wannan dan kudi da take juyawa da shi take kula da kanta da kuma daukar nauyin 'ya'yanta guda biyu.

Ba a bayyana ko matar tana da miji ba ko kuma abinda ya faru da mahaifin yaran nata guda biyu ba, amma a yadda tayi magana ya nuna cewa babu wani namiji da yake kula da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel