Annobar cutar corona ta harbi wani babban dan kwallon Juventus
Kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta sanar da tabbacin kamuwar wani dan kwallonta mai suna Daniele Rugani da mugunyar cutar nan ta shaker iska, watau Coronavirus wanda a yanzu ta addabi kasashen Duniya.
Juventus ta bayyana haka ne a ranar Laraba, 11 ga watan Maris, inda ta ce har zuwa yanzu dai Rugani bai fara nuna wata alamar kamuwa da cutar ba, amma gwajin da aka masa ya tabbatar yana dauke da kwayar cutar a jikinsa.
KU KARANTA: Mutuwa ta yi awon gaba da hadiman gwamna guda 3 cikin kwanaki 5
Wannan yasa kungiyar ta dauki matakin killace shi don gudun yaduwar cutar a tsakanin yan wasanta, yan kallo da kuma sauran ma’aikatanta, kamar yadda mahukunta kungiyar suka tabbatar.
“Dan kwallonmu, Daniele Rugani ya kamu da cutar Coronavirus-COVID-19, amma a yanzu bai riga ya fara nuna alamun cutar ba, a yanzu haka hukumar Juventus ta dauki matakan killace shi kamar yadda tsare tsare suka tanada, har ma da wadanda suka yi mu’amala dasu.”
Zuwa yanzu dai Rugani ne wani babba kuma fitaccen dan kwallo da ya kamu da cutar Coronavirus. A yanzu haka dai an dage wasu wasannin kwallo a nahiyar turai, yayin da aka buga wasu wasannin ba tare da gayyatar yan kallo ba duk don gudun yaduwar cutar.
An daga kwantan wasan kungiyar Arsenal da Manchester City har sai baba ta ji sakamakon bullar cutar Corona a kasar Ingila, haka zalika wasan kungiyar PSG da Dortmund a gasar zakarun nahiyar turai wanda aka buga shi a kasar Faransa a daren Laraba bai samu halarcin yan kallo ba.
Idan za’a tuna, Matashin dan kwallon Najeriya dake taka leda a kasar Italiya, mai suna King Paul Akpan Udoh ya kamu da mugunyar cutar nan ta Coronavirus, Paul ne dan kwallo na farko daya fara kamuwa da wannan cutar.
A ranar 27 ga watan Feburairu aka fara gano cutar a tattare da shi, kuma tun daga nan aka kebance shi daga jama’a. shi dai Paul mai shekaru 22 ya fara kwallonsa ne a kungiyar Reggiana, daga nan ya koma Juventus a shekarar 2011, a shekarar 2019 Paul ya koma Pianesa.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng