Jami’an tsaro guda 40 ne suke tsaron tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi a Nassarawa

Jami’an tsaro guda 40 ne suke tsaron tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sunusi a Nassarawa

Gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana cewa ita bata fatattaki tsohon Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sunusi zuwa jahar Nassarawa ba.

Mukhtar yace fatattakar sarki daga Kano baya cikin umarnin gwamnatin, ya kara da cewa sun dai dauke shi ne kawai daga garin Kano ta hanyar amfani da Yansanda saboda wasu bayanan sirri da suka samu.

KU KARANTA: Mutuwa ta yi awon gaba da hadiman gwamna guda 3 cikin kwanaki 5

Sai dai jaridar Punch ta ruwaito a ranar Laraba, 11 ga watan Maris cewa an kara adadin jami’an tsaron dake tsare da tsohon Sarki mai murabus a gidan da yake zaman hijira a garin Awe na jahar Nassarawa.

Babban lauyan jahar, kuma kwamishinan sharia na jahar, Ibrahim Mukhtar ne ya bayyana haka cikin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channles, inda ya bayyana cewa abin da gwamnati ta yi kawai shi ne tsige shi daga mukaminsa saboda rashin da’a.

“Idan ka saurari jawabin sakataren gwamnatin jahar Kano game da tsige sarkin, babu inda ya yi nuni da cewa an fatattaki sarkin daga jahar, hukuncin da gwamnati ta dauka kawai shi ne tsige shi, tare da sanar da sabon sarki.” Inji shi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin jami’an hukumomin tsaro da suka mamaye gidan da ake tsare da Sunusi a Awe akwai Yansanda, jami’an Civil Defence, da kuma na hukumar leken asiri, DSS, wanda suke ta karar duk wanda ya nufo gidan da nufin ganin Sarkin.

Daga cikin wadanda jami’an suka hana ganin tsohon sarkin akwai manyan sarakuna guda biyu da suka hada da Yakanajin Uke, Alhaji Ahmad Abdullahi da kuma Sarkin Karshi, Dakta Muhammad Bako.

A hannu guda kuma, gwamnan jahar Kaduna, kuma abokin tsohon Sarkin, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya nada Sunusi a matsayin sabon shugaba kuma uban jami’ar jahar Kaduna, gwamnan ya sanar da nadin ne a ranar Laraba, 11 ga watan Maris.

Wannan nadi ya biyo bayan nadin da gwamnatin jahar Kaduna ta yi ma Sunusi a ranar Talata, 10 ga watan Maris ne inda ta nada shi mukamin mataimakin kwamitin gudanarwa na hukumar zuba hannun jari a jahar Kaduna.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel