Babban burina shine na kwanta akan katifa kafin na mutu - Cewar wata tsohuwa
- Yara Kwanjit, wata tsohuwa daga Saanbona a yankin arewa maso gabashin kasar Ghana ta bayyana cewa babban burinta shine ta kwanta akan katifa kafin ta mutu
- A cewar Yara wacce take talaka ce kuma ba ta gani, ta ce bata samu irin rayuwar da take so ba, saboda akwai raneku da yawa da ko abinci ba ta iya samu ta ci saboda babu
- Yara ta bayyana cewa tana da yara biyu amma dukkansu sun koma kudancin Ghana da zama
Wata tsohuwa wacce ba ta gani mai suna Yara Kwanjit dake Saanbona a yankin arewa maso gabashin kasar Ghana ta bayyana babban burinta a rayuwa, inda ta bayyana cewa abinda tafi so a yanzu shine ta kwanta akan katifa.

Asali: Facebook
A wani bidiyo da JoyNews ta yi ya nuna tsohuwar wacce ba ta san ainahin shekarunta ba, da kuma take da 'ya'ya guda wadanda basa zaune tare da ita.
A yadda Yara ta bayyana, 'ya'yanta guda biyun duka sun gudu yankin kudancin kasar Ghana domin su cigaba da zama a can, kuma duka a cikin 'ya'yan nata guda biyu daya ne kawai yake kawo mata ziyara.
A wata hira da aka yi da tsohuwar ta bayyana cewa ta makance bayan ta haifi danta na biyu, kuma ta bayyana cewa ta san da ace tana da kudida tuni har yanzu tana gani.
Ta ce ta san duk da cewa ba ta san yawan shekarunta ba, amma ta san bai kamata ace tayi irin tsufan da tayi yanzu ba, ta san cewa tsufanta yana da nasaba da rashin kudi.
A yadda take Yara ta bayyana cewa akwai raneku da yawa da suke zuwa su wuce ba tare da taci abinci ba, ta ce zama talaka yana nufin rashin samun abinda mutum yake so a rayuwa.
Yara ta ce abinda tafi so a rayuwarta yanzu kafin ta mutu shine ta kwanta akan katifa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng