Majalisar Dinkin Duniya ta dauke shi aiki, bayan ya nemi aiki sau 500 a wajen bai samu ba

Majalisar Dinkin Duniya ta dauke shi aiki, bayan ya nemi aiki sau 500 a wajen bai samu ba

- Momo Bertrand saurayi ne dan asalin kasar Kamaru da ya bawa duniya mamaki da irin abinda yayi na jajircewa

- Momo dai ya nemi aiki a majalisar dinkin duniya har sau 500 bai samu ba, amma hakan bai sanya ya saduda ba

- A karshe dai majalisar ta dauke shi aiki a fannin sadarwa, hakan ya sanya shi wallafa labarin shi a yanar gizo

Wani saurayi mai suna Momo Bertrand ya ce yanzu shi kakarshi ta yanke saka, bayan Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta dauke shi aiki, bayan ya nemi aiki sau 500 a wajen bai samu ba.

Bertrand dai ya wallafa hakan ne a shafinsa na LinkedIn, inda yake cewa ya fara neman aiki a Majalisar Dinkin Duniya tun lokacin da ya kammala karatunsa na digiri na biyu.

TUKO.co.ke ta gano cewa Bertrand ya bayyanawa 'yan ajinshi cewa su nemi aiki a Majalisar Dinkin Duniya, amma maimakon su goya masa baya sai suka fara yi masa dariya suna cewa yaje ya nemi aikin koyarwa kawai shine zai fi masa.

Bertrand wanda yake dan asalin birnin Douala ne dake kasar Kamaru, ya ce bai tsaya ya saurari abinda abokanan shi suke ce masa ba na rashin bashi karfin guiwa akan ya ce musu yana so yayi aiki da Majalisar Dinkin Duniya.

"Na taba gayawa wani abokina dan ajinmu, amma sai ya fara yi mini dariya, ya ce Momo Majalisar Dinkin Duniya ba za ta dauke ka aiki ba saboda babu wanda ka sani a wajen. Maimakon haka mai zai hana ka nemi aikin malamin makaranta a nan San Diego," ya ce.

"Ban saurare shi ba. Bayan na nemi aikin sau 500 ban samu ba, yanzu an dauke ni aiki a bangaren sadarwa a Majalisar Dinkin Duniya," Momo ya kara da cewa.

Wannan abu da ya wallafa ya karawa mutane da yawa karfin guiwa inda suka dinga yi masa san barka da irin wannan jajircewa da yayi.

Wasu ma sun ce sun samu karfin guiwar yin aiki tukuru domin ganin sun samu abinda suke so duk da irin kalubalen da zasu dinga fuskanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel