Ganduje ya bawa sabbin sarakunan Kano da Bichi takardar kama aiki

Ganduje ya bawa sabbin sarakunan Kano da Bichi takardar kama aiki

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya mika takardun kama aiki ga Aminu Ado Bayero da Nasiru Ado Bayero a matsayin sabbin sarakunan masarautun Kano da na Bichi.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa an nada Aminu Ado Bayero ne bayan Gwamnan ya tube rawanin Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano a ranar Litinin. Ya kara da nada Nasiru Ado Bayero ne sakamakon gurbin da Aminu Ado Bayero ya bari a masarautar Bichi.

A yayin jawabin Sarkin bayan karbar takardar kama aikin a gidan gwamnatin jihar Kano, ya ce a matsayinsa na Musulmi, ya yadda da kaddara da kuma ikon Allah. Hakazalika Allah baya kuskure ko kadan.

Kamar yadda ya sanar “Mun yadda cewa komai na da karshe. Dole ne mu tuna da marigayin tsohon sarki Ado Bayero, wanda yace mu kiyaye tare da tsoron Allah. Ya horar damu a kan hakuri da biyayya ga na gaba.”

Ya jaddada mana abinda hakuri zai iya haifarwa. A yanzu ne muka ga amfanin horarwar da ya yi mana. Ina kira ga jama’a ta da su ji tsoron Allah kuma su kaunaci juna don kawo ci gaba ga masarautar, jihar Kano da kuma Najeriya baki daya,” yace.

Ganduje ya bawa sabbin sarakunan Kano da Bichi takardar kama aiki
Ganduje ya bawa sabbin sarakunan Kano da Bichi takardar kama aiki
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Sarkin Loko ya bayyana abinda suka tattauna da Sanusi II a daren da ya kwana a garinsa

Sabon sarkin ya kara da mika godiyarsa ga Ganduje da kuma masu nada sarki da suka zabe shi. Ya yi alkawarin tabbatar da gado da kuma wanzar da abinda magabata suka kafa.

Sarki Aminu, wanda yake jawabi cikin hawaye, ya yi alkawarin goyon bayan gwamnatin Ganduje da kuma shugaban kasa Muhammmadu Buhari.

A yayin jawabinsa, sabon sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero ya mika godiyarsa ga Allah da ya nuna masa wannan ranar.

“Muna godiya ga Allah da kuma gadon kakanninmu. Muna addu’ar rahamar Ubangiji ta tabbata a garesu kuma ya hada mu a ranar kiyama,” yace.

A yayin jinjinawa Gwamna Ganduje a kan ilimi kyauta kuma na dole, Sarki Nasiru yayi kira ga gwamnan da ya samar da karin guraben ayyuka ga matasa marasa aikin yi a jihar.

Ya kara da jaddada cewa zai sauke nauyin da aka dora masa na tabbatar da ci gaban masarautar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel