Yadda aka ci zarafin Sanusi da iyalansa kafin su bar fada - Lauyansa

Yadda aka ci zarafin Sanusi da iyalansa kafin su bar fada - Lauyansa

Shugaban lauyoyin tubabben sarkin Kano, Abubakar Balarabe Mahmoud, ya yi bayanin yadda Malam Muhammadu Sanusi II da iyalansa suna fuskanci cin zarafi bayan an tube masa rawaninsa.

Balarabe Mahmoud, tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya, ya ce kafin Sanusi ya samu wasikar tube masa rawani, an samu hargitsi a sashin iyalan mai martaban domin kuwa wasu mutane da bai dace ba sun so shiga sashin iyalan mai martaban.

Babban lauyan ya ce, "Wannan lamarin yayi kamari don har barkonon tsohuwa aka watsa. Hankula sun kwanta ne bayan da wadannan mutanen suka janye daga yunkurin shiga sashin iyalan mai martabar."

Ya ce tsohon gwamnan bankin Najeriya din daga bisani ya samu wasikar da ke bayyana cewa ya gaggauta komawa jihar Nasarawa.

Balarabe Mahmoud ya ce, "Mun bukaci sanin cewa ko an kama shi ne kuma muna bukatar ganin shaidar hakan. Amma sai kwamishinan 'yan sandan ya tabbatar mana da cewa ba kama shi aka yi ba. Mun sanar da kwamishinan 'yan sandan cewa wannan ya take hakkinsa da kundun tsarin mulki ya bashi don za a mayar dashi ne babu yardarsa."

Yadda aka ci zarafin Sanusi da iyalansa - Lauyansa
Yadda aka ci zarafin Sanusi da iyalansa - Lauyansa
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Buhari da gwamnan Nasarawa suna ganawa a Aso Rock

"Sarkin ya bayyanawa kwamishinan 'yan sandan cewa abokansa sun turo jirgin da zai daukesa tare da iyalansa zuwa jihar Legas. Kawai yana bukatar tsaro ne a filin jirgin don ya bar garin. Kwamishinan kuwa ya hana hakan tare da tabbatar da cewa umarni ne aka bashi. Za su bar iyalansa su tafi Legas amma shi kuwa za a kaishi Abuja daga nan ya wuce Nasarawa." Yace.

Ya ce, a lokacin da ya bayyana cewa 'yan sandan za su yi amfani da karfi ne a kan sarkin, sai ya basu hadin kai don kada shi da iyalansa su fada halin rashin tsaro.

Balarabe Mahmoud yace sarkin ya shiga jirgin saman da aka kawo ne da karfe 6:40 na yamma yayin da iyalansa suka yi amfani da jirgin da abokan sarkin suka turo zuwa jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel