Rikici tsakanin jama’an gari da jami’an kwastam ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4

Rikici tsakanin jama’an gari da jami’an kwastam ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 4

Akalla mutane hudu ne suka mutu a hannun jami’an hukumar yaki da fasa kauri, watau kwastam a garin Ibadan na jahar Oyo biyo bayan wata rikici data balle sakamakon kama wata motar fasa kauri da jami’an hukumar suka yi.

Premium Times ta ruwaito wasu mazauna yankin sun bayyana cewa mutanen sun mutu ne yayin da suke gudanar da zanga zanga don nuna bacin ransu game da kwace wata mota da kwastam ta yi, sai dai wasu kuma sun ce mutanen sun mutu a sanadiyyar bugesu da motar ta yi bayan kwastam ta kwace ta.

KU KARANTA: Kowa da matsalarsa: Matashi ya kama hanya a kasa don jinjina ma Sarkin Kano Aminu daga Jigawa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an gudanar da zanga zangar ne a gaban barikin jami’an kwastam dake Ijokodo na garin Ibadan, hakanan rikicin ya samo asali ne bayan jami’an kwastam sun kama wata babbar mota dake dauke da kayan fasa kauri.

Bayan sun kwace motar shi ne suka motar da nufin kai ta cikin barikinsu domin cigaba da gudanar da bincike, suna cikin tafiya ne sai birnin motar ya shanye, hakan tasa motar ta kufce ma jami’in kwastam dake tukar motar, daga nan ya bi ta kan mutane.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa daga cikin wadanda lamarin ya shafa akwai wani dan achaba, wannan ne yasa abokansa yan achaba suka niki gari zuwa barikin kwastam don nuna bacin ransu, daga nan kuma sai jami’an hukumar suka bude ma masu zanga zangar wuta, nan take suka kashe mutane 4, daga ciki har da wata mata.

Sai dai mai magana da yawun hukumar Yansandan jahar Oyo, Olugbenga Fadeyi ya bayyana rashin wata masaniya dangane da aukuwar lamarin, amma mai magana dayawun hukumar kwastam na jahar Oyo, Abdullahi Legas ya tabbatar da aukuwar lamarin.

A cewar Abdullahi, sun garzaya da mutanen da lamarin ya shafa zuwa babban asibitin koyarwa na jami’an Ibadan, kuma suna tare da iyalan mutanen da lamarin ya shafa, don haka ba zai iya cewa komai ba har sai ya kammala tattara rahoto.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng