Buhari ne ya bayar da umarnin tumbuke Sarkin Kano – Kwankwaso

Buhari ne ya bayar da umarnin tumbuke Sarkin Kano – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jahar Kano, kuma wanda ya nada tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa tubuke rawanin Sarkin Kano umarni ne daga wajen shugaban kasa Muhammadu Buhari.

BBC ta ruwaito Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da ya yi da ita game da batun tsige tsohon Sarkin na Kano, inda ya bayyana hakan a matsayin abin bakin ciki ga jahar Kano, Najeriya da ma duniya gaba daya.

KU KARANTA: Kowa da matsalarsa: Matashi ya kama hanya a kasa don jinjina ma Sarkin Kano Aminu daga Jigawa

A cewar Kwankwaso: "Shuwagabannin gwamnatin Kano da kansu ne su ke cewa umarni aka ba su, kuma shi ya ba su umarni….Shugaba Buhari yana tsoma hannu cikin al'amuran jihar Kano, Inda ya kamata ya sa hannun sai mu ga ba nan ya sa hannu ba, inda kuma bai kamata ya sa hannu ba, sai mu ga a nan ya sa hannu….sai dai musamman mu nan a Kano yadda muke gani yana hargitsa inda yake sa hannu".

Haka zalika Kwankwaso ya musanta zargin da ake yadawa na cewa wai tun yana gwamna ya taba baiwa tsohon Sarkin takardar gargadi har sau uku sakamakon irin furucin da yake furtawa, inda yace; “Ni ban taba ba Mai martaba sarki wata takardar gargadi ko ma wani abu irin wannan ba".

Game da zargin da ake masa tare da magoya bayansa yan Kwankwasiyya game da rura rikicin dake tsakanin Gwamna Ganduje da tsohon Sarkin Kano kuwa, Kwankwaso ya ce su a kullum suna bayan mai gaskiya ne.

Sa’annan ya bayyana cewa babban abin da yasa sarkin ya gamu da fushin Gwamna Ganduje bai wuce bukatar da ya bayyana ba na cewa a baiwa duk wanda ya ci zaben gwamnan Kano nasararsa.

A wani labari kuma, wani matashi mai ji da kardi daga jahar Jigawa ya kaddamar da tattaki zuwa jahar Kano domin taya sabon Sarkin Kano, mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero murnar darewar karagar mulki.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan matashi mai suna Umar dan asalin jahar Kano ne, amma yana karatu a jami'ar gwamnatin tarayya dake birnin Dutse na jahar Jigawa.

Murna da farin ciki da ya turnuke Umar biyo bayan sanar da Aminu Ado a matsayin sabon Sarkin Kano ne yasa ya fara wannan tattaki domin yin jinjinar ban girma, tare da bayyana ma sabon sarkin farin cikinsa da kuma fatan alheri.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel