Bayan shekaru yana mai gadi a wani kamfani, yanzu ya mallaki kamfanin kanshi na man fetur
- Wani matashi da ya kwashe shekaru da yawa yana aikin gadi a wani kamfani, yanzu kakarsa ta yanke saka
- Matashin yanzu ya kafa kamfanin man fetur na shi bayan barin aikin gadin
- Matashin dan kasar Kamaru ya shawarci mutane da kada su cire rai akan duk abinda suka sanya a gaba
Wani matashi mai suna AD Patrickson ya bayyana wani labari na shi mai kayatarwa akan yadda ya zama mamallakin kamfanin man fetur, bayan shafe shekaru masu yawa yana aikin gadi a wani kamfani.

Asali: Facebook
Patrickson ya ce domin gani ya cimma wannan buri na shi, sai da ya bar komai da komai ya mayar da hankali akan aikin na shi. Ya kara da cewa soyayyar da yake yiwa wannan abu da ya sanya a gaba, ita ce ta sanya ya kai wannan matsayi.
Yanzu da komai ya kankama, ya zama shugaba kuma mamallakin kamfanin man fetir na Source Rock, kamfanin farko a kasar Kamaru da yake harkar man fetur ba tare da taimakon kwararru ba.
A bayanin da yayi na karshe a shafinsa na LinkedIn, Patrickson ya karawa mutane kwarin guiwa, musamman wadanda suke da mafarki irin na shi, inda ya ce musu kada su hakura da duk abinda suka sanya a gaba, ya ce hakuri shine mafarin komai.
KU KARANTA: Bayan shafe shekaru 17 a matsayin manyan abokai, sun gano cewa yaya da kanwa ne
Haka a makon da ya gabata mun kawo muku labarin wani matashi da ya shafe shekaru masu yawan gaske yana neman aiki ya rasa, amma a karshe ya kafa sana'arshi.
Matashin bayan kammala karatun shi ya nemi aiki sau 200 amma ya rasa, kawai sai ya fara sana'ar kiwon kaji, cikin ikon Allah kuma sana'ar ta samu karbuwa.
Yanzu haka dai saurayin wanda yake dan asalin kasar Ghana yana samun sama da naira miliyan hudu a wata da wannan sana'a ta kiwon kaji.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng