Barawo ya shiga ofishin 'yan sanda yayi awon gaba da talabijin da suke kallo da ita

Barawo ya shiga ofishin 'yan sanda yayi awon gaba da talabijin da suke kallo da ita

- Wani barawo da har yanzu ba a san ko waye ba ya sidada cikin ofishin 'yan sanda yayi awon gaba da wata katuwar talabijin da suke kallo da ita

- Barawon dai ya shiga ofishin ne da cikin dare a lokacin da 'yan sandan suke kan bakin aiki, inda ya dauke talabijin din ba tare da wani ya ganshi ba

- Talabijin din dai an bayyana cewa kyauta ce kamfanin Startimes ya yiwa ofishin 'yan sandan domin girmamawa, sai kuma wannan lamari ya zo ya faru

Jami’an ‘yan sanda na babban ofis na Jinja dake kasar Uganda suna binciken wani lamari da ya faru, na yadda aka sace wata talabijin da take a cikin ofishin nasu, wacce aka ba su ita kyauta makonni kadan da suka gabata.

Talabijin din mai girman inci 40 da kamfanin Startimes ta basu kyauta a watan Disambar 2019, an neme ta sama da kasa an rasa a ranar 13 ga watan Janairun wannan shekarar.

A yadda rahoto ya bayyana, yayin da ‘yan sanda suke tunanin sun ajiye talabijin din inda baza a samu wata matsala ba, wani dan sanda wanda yaki bari a bayyana sunan shi, ya ce sun wayi gari da safe sun nemi talabijin din sun rasa.

“Talabijin din kamfanin Startimes ne ya bamu ita a watan Disamba, kuma mun saka ta a cikin ofishin mu, amma mun neme ta sama ko kasa mun rasa, kuma bamu san waye ya dauka ba,” cewar dan sandan.

KU KARANTA: Satar sadakar coci: 'Yan sanda sun kama mata mai shekaru 24

Kakakin rundunar ‘yan sandar ta yankin Kiira, Diana Nandaula, ta tabbatar da faruwar lamarin:

“Tabbas an sace talabijin din, kuma mun bukaci jami’an ‘yan sandan da suke aiki a lokacin da su yi bayanin abinda ya faru,” ta ce.

A wani bangare kuma, wani barawo ne shi kuma ya da aka kamo shi aka kulle shi a cikin ofishin 'yan sandan ya samu ya kubce ya kuma gudu da littafin da suke daukar rahoton masu laifi baki daya.

Tun guduwar shi dai har yanzu 'yan sandan sun bayyana cewa basu sake jin duriyar shi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel