Na kama matata tana zina da maza har sau 8 - Magidanci ya sanar da kotu

Na kama matata tana zina da maza har sau 8 - Magidanci ya sanar da kotu

Abdullahi Olabamaji dai mai aski ne kuma mazaunin Ibadan. A jiya ne ya sanar da wata kotun gargajiya da ke Ibadan, jihar Oyo halin da yake ciki da matarsa.

Ya ce matarsa mai suna Yetunde ba ta da kamun kai kuma ya kama ta da a kalla maza takwas tana cin amanarsa.

Olabamiji dai mazaunin yankin Ojo ne kuma ya sanar da hakan ne a gaban mai shari'a Ademola Odunade na kotun.

Ya sanar da cewa, daya daga cikin kwartayen matar shi na da karfin halin hallara a wani sha'anin iyalinsa. "Mai shari'a, a yayin da Yetunde ta tsunduma cikin aikata miyagun al'amura, nayi kira ga iyayenta da sauran 'yan uwanta amma kullum sai dai su ce inyi hakuri."

"Wata rana, bayan Yetunde ta gudu ta barni na dan lokaci kamar yadda ta saba, naje gidan iyayenta don tattaunawa dasu. Na sha mamakin gaske da naga matata a kan cinyar wani gardi. A nan ne nasan iyayenta sun san abinda take yi." ya ce.

Matata tayi zina da maza takwas - Magidanci ya sanar wa kotu

Matata tayi zina da maza takwas - Magidanci ya sanar wa kotu
Source: UGC

DUBA WANNAN: Buri na na karshe a rayuwa shine in mutu a kan kujerar sarautar Kano - Sanusi II

Ya kara da cewa, "Ta saba tozarta ni kuma bana son yara na su tashi da miyagun dabi'unta."

Yetunde, mazauniyar yankin Foko da ke Ibadan kuma madinkiya, ta maka mijinta a kotu da bukatar a raba su don yana barazana ga rayuwarta. Ta ce halin masifar mijinta ya isheta.

An rufe ta a gidan gyaran hali har sau uku. Ta zargi cewa, "rayuwata tana cikin hatsari a tare dashi saboda koyaushe yana barazanar halaka ni. Yana satar kudina kuma yana cin zarafin iyayena."

Ta roki kotun da ta bata yaranta.

Mai shari'a Odunade ya kashe auren a take saboda zaman lafiya ya wanzu. Ya ba Olabamiji rikon yaran sannan ya bukaci Yetunde da ta garzayo kotu a duk lokacin da ta bukaci ganin yaranta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel