Kano: Sabon sarki ya garzaya gaban mahaifiyarsa don neman tabarraki

Kano: Sabon sarki ya garzaya gaban mahaifiyarsa don neman tabarraki

- A yau Talata ne sabon Sarkin Kano, Aminu Bayero ya ziyarci makabartar da sarakunan Kano ke kwance a gidan sarki da ke Nassarawa

- Aminu Bayero ya ziyarci makabartar da sarakunan Kano ke kwance ne don yin adu’o’i ga mahaifinsa marigayi Alhaji Ado Bayero

- Sabon Sarkin ya kara da garzayawa zuwa wajen mahaifiyarsa da ke unguwar Gandun Albasa domin neman tabaraki garesa da sauran hakiman Kano

A yau Talata ne sabon Sarkin Kano, Aminu Bayero ya ziyarci makabartar da sarakunan Kano ke kwance a gidan sarki da ke Nassarawa don yin adu’o’i ga mahaifinsa marigayi Alhaji Ado Bayero.

Sabon Sarkin ya kara da garzayawa zuwa wajen mahaifiyarsa da ke unguwar Gandun Albasa domin neman tabaraki garesa da sauran hakiman Kano da suka yi mubaya’a.

Ya kara da biyowa ta titin gidan Zoo daga nan ya wuce gidansa da ke Mandawari duk a cikin birnin Kanon.

Kamar yadda gidan rediyon Freedom da ke Kano ta ruwaito, jama’ar jihar Kano da kuma jami’an tsaro ne suka raka sabon sarkin wajen mahaifiyarsa.

Kano: Sabon sarki ya garzaya gaban mahaifiyarsa don neman tabaraki

Kano: Sabon sarki ya garzaya gaban mahaifiyarsa don neman tabaraki
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan yadda Kanawa suka yi tururuwa zuwa gidan sabon sarki don taya shi murna

Amma kuma, A yau Litinin 10 ga watan Maris ne al'ummar Kano da dama suka yi tururuwa zuwa gidan sabon sarkin Kano Aminu Ado Bayero domin taya shi murnar nadin da aka masa a matsayin sarki.

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya nada Aminu Ado Bayero ne bayan ya cire tsohon sarki Muhammadu Sanusi II a kan dalilan rashin yi wa gwamnati da'a. Mutanen sun isa gidan suna kirari da wakoki na murnar nada sabon sarki a Kano.

Daga bisani, sabon Sarki Aminu Ado Bayero ya ziyarci ya fito daga gida ya tafi gidan Nasarawa inda kaburburan kakakansa da mahaifinsa su ke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel