An garzaya da tsohon sarkin Kano zuwa sabon gidan da zai zauna a Awe

An garzaya da tsohon sarkin Kano zuwa sabon gidan da zai zauna a Awe

Tsohon Sarkin Kano mai murabus, Muhammadu Sunusi II ya isa gidansa dake garin Awe, cikin karamar hukumar Awe ta jahar Nassarawa biyo bayan tumbuke shi da gwamnatin jahar Kano a karkashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta yi.

Idan za’a tuna gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ce ta sanar da tsige Muhammadu Sunusi a ranar Litinin, 9 ga watan Maris ta hannun sakataren gwamnatin jahar Alhaji Usman Alhaji.

KU KARANTA: Babu gwamnatin da zata zura ido ana sukarta kamar yadda Sunusi yake yi – Hadimin Ganduje

An garzaya da tsohon sarkin Kano zuwa sabon gidan da zai zauna a Awe
An garzaya da tsohon sarkin Kano zuwa sabon gidan da zai zauna a Awe
Asali: Facebook

Gwamnatin ta bayar da hujjojinta guda uku wanda ta bayyana su ne suka sabbaba gwamnan daukan mataki mai tsauri a kan Sarkin da suka hada da rashin da’a, kin halartar zaman tattaunawa da kuma karya dokokin masarautar Kano, kamar yadda sakataren gwamnatin jahar Kano ya bayyana.

Sai dai tuni gwamnatin ta sanar da tsohon Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano, yayin da dan uwansa Nasiru Ado Bayero ya zama sabon Sarkin Bichi.

Da fari an fara zarcewa da tsohon Sarkin babban birnin tarayya Abuja, daga bisani aka wuce da shi zuwa wani gida a kauyen Loko dake cikin karamar hukumar Nassarawa na jahar Nassarawa, sai dai a yanzu an mayar da shi zuwa wani gida a garin Awe.

An garzaya da tsohon sarkin Kano zuwa sabon gidan da zai zauna a Awe
An garzaya da tsohon sarkin Kano zuwa sabon gidan da zai zauna a Awe
Asali: Facebook

Daily Nigerian ta ruwaito shugaban ma’aikatan Sarki Sunusi, Munir Sunusi ne ya bayyana mata a ranar Talata, inda yace sun isa fadar gwamnatin jahar Nassarawa, inda daga nan zasu zarce karamar hukumar Awe inda aka baiwa Sunusi sabon gida.

Kwamishinan Yansandan jahar Nassarawa, Bola Longe tare da shugaban hukumar tsaron farin kaya ta jahar sun riga zuwa fadar gwamnatin jahar domin tarbar Sunusi.

Rahotanni sun bayyana manyan mutane kamar su Aliko Dangote da Janar Ali Gusau sun nemi gwamnan ya sauya ma Sunusi wurin zama sakamakon kauyen Loko na da wahalar shiga saboda rashin hanya mai kyau, kuma Awe ta fi Loko zama birni.

Wannan sabon gida da aka kai Sarkin mallakin shugaban karamar hukumar Awe ne, kuma dakuna biyu ne a ciki kacal, Sunusi ya samu rakiyar Sarkin Lafi,a Sidi Bage da Sarkin Awe Isa Umar II.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng