Ba’a nan take ba: Sanusi zai iya komawa kujerarsa – inji babban lauyansa

Ba’a nan take ba: Sanusi zai iya komawa kujerarsa – inji babban lauyansa

Babban lauyan tsohon Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II, Abubakar Mahmoud SAN ya bayyana cewa tsohon Sarkin zai iya komawa kujerarsa idan ya tafi kotu, domin kuwa kotu na da ikon soke tsigewar da aka yi masa.

Idan za’a tuna gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ce ta sanar da tsige Muhammadu Sunusi a ranar Litinin ta hannun sakataren gwamnatin jahar Alhaji Usman Alhaji.

KU KARANTA: Muhammadu Sunusi mai murabus ya koma kauyen Loko a jahar Nassarawa

Ba’a nan take ba: Sanusi zai iya komawa kujerarsa – inji babban lauyansa

Ba’a nan take ba: Sanusi zai iya komawa kujerarsa – inji babban lauyansa
Source: Facebook

Gwamnatin ta bayar da hujjojinta guda uku wanda ta bayyana su ne suka sabbaba gwamnan daukan mataki mai tsauri a kan Sarkin da suka hada da rashin da’a, kin halartar zaman tattaunawa da kuma karya dokokin masarautar Kano, kamar yadda sakataren gwamnatin jahar Kano ya bayyana.

Sai dai tuni gwamnatin ta sanar da tsohon Sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero a matsayin sabon Sarkin Kano, yayin da dan uwansa Nasiru Ado Bayero ya zama sabon Sarkin Bichi.

Amma lauyan Sunusi yace basu kai ga daukan mataki ba, koda yake ya bayyana cewa basu yi mamakin tsige Sarkin ba, amma yace abin kunya ne yadda aka tsige shi ba tare da bashi daman kare kansa ba, kamar yadda ya bayyana ma jaridar Punch.

“Ya sha fama da gwamnatin jahar Kano a gaban kotuna daban daban a cikin shekaru biyu zuwa uku da suka gabata, don haka wannan bai bamu mamaki ba, amma mun ji kunyar yadda aka tsige shi ba tare da bashi daman kare kansa ba.

“Duk da haka gwamnati ta sanar da tsige shi, kuma har an dauke shi zuwa Abuja, zamu samu daman ganawa da shi domin tattauna matakin daya kamata mu dauka a matsayinmu na lauyoyinsa, kuma muna da yakinin haramtacciyar tsigewa aka masa.

“Musamman ma maganan sallamarsa daga garin, a kundin tsarin mulkin Najeriya babu wanda ya isa ya hanaka yancin zirga zirga, amma dai duka wannan sai mun tattauna da shi tukunna tare da samun umarninsa, maganan guda biyu ne tsige shi da kuma korarsa daga gari.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel