Muhammadu Sunusi zai koma jahar Nassarawa don cigaba da rayuwarsa

Muhammadu Sunusi zai koma jahar Nassarawa don cigaba da rayuwarsa

Sarkin Kano mai murabus, Malam Muhammadu Sunusi II zai koma jahar Nassarawa domin cigaba da rayuwarsa bayan tsige shi daga kujerar sarautar Kano da gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi.

Jaridar Daily Sun ta ruwaito wata majiya ta karkashin kasa daga fadar Sarkin Kano ta tabbatar mata da cewa zuwa lokacin tattara rahoton nan Sarkin tare da iyalansa sun fara tattara komatsansu da nufin ficewa daga fadar tare da sa idon jami’an tsaro.

KU KARANTA: Zaratan matasa yan sa kai sun kubutar da mutum 2 daga hannun yan bindiga a Katsina

Jami’an tsaro da suka hada da Yansanda da na hukumar DSS sun yi masa rakiya har zuwa filin sauka da tashin jirage na jahar Kano, daga nan kuma zasu raka shi zuwa wani gari da ba’a bayyana sunansa ba a jahar Nassarawa don cigaba da rayuwarsa.

Idan za’a tuna gwamnatin jahar Kano a karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje ce ta sanar da tsige Muhammadu Sunusi a ranar Litinin ta hannun sakataren gwamnatin jahar Alhaji Usman Alhaji.

Sai dai gwamnatin ta bayar da hujjojinta guda uku wanda ta bayyana su ne suka sabbaba gwamnan daukan mataki mai tsauri a kan Sarkin da suka hada da rashin da’a, kin halartar zaman tattaunawa da kuma karya dokokin masarautar Kano, kamar yadda sakataren gwamnatin jahar Kano ya bayyana.

A hannu guda kuma ana gwamnan jahar Kano zai sanar da sabon Sarkin Kano a yau Litinin, 9 ga watan Maris bayan ya tsige Muhammadu Sunusi II a matsayin Sarkin Kano.

Wani babban jami’in tsaro da ya halarci ganawar tsaro na gaggawa da gwamnan jahar Kano ya kira a fadar gwamnati ya bayyana cewa zuwa yammacin yau gwamnati za ta nada sabon Sarki.

A wani labarin kuma, manyan fadawan masarautar Kano guda hudu sun isa fadar gwamnatin jahar Kano domin tattaunawa da Gwamna Ganduje kafin sanar da sunan sabon Sarkin Kano.

Manyan masu nadin Sarkin sun hada da Madakin Kano, Yusuf Nabahani, Makaman Kano Sarki Abdullahi, Sarkin Dawaki Mai Tuta Abubakar Tuta da Sarkin Bai Mukhtar Adnan.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel