Babu bata lokaci: Tubabben Sarkin Kano ya kammala shirin barin fada, zai bar Kano

Babu bata lokaci: Tubabben Sarkin Kano ya kammala shirin barin fada, zai bar Kano

Tsohon sarkin Kano da gwamnatin ta tube wa rawani a ranar Litinin, Muhammadu Sanusi II, zai bar jihar Kano a yau, Litinin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa cewa majiyarta ta tabbatar mata.

Kazalika, majiyar ta sanar da Daily Trust cewa tuni gungun jami'an tsaro suka kwace iko da fadar gabanin fitar da Sanusi daga jihar Kano.

Sai dai, a wani labarin da Legit.ng ta samu daga shafin jaridar BBC Hausa na nuni da cewa tuni an fitar da Sanusi daga fadar Kano, kuma za a raka shi ya hau jirgi don barin Kano.

Kwamishinan yada labaran jihar Kano, Muhammed Garba, ya tabbatar wa da BBC cewa an bawa Sanusi tsaro, a saboda haka ba ya fuskantar wata barazana a yayin da za a raka shi wurin da zai zame masa mafaka bayan fitar da shi daga fadar sarkin Kano.

Rundunar jami'an tsaro a ranar Litinin ta tsinkayi fadar Sarkin Kano da ke jihar Kano. Wannan ya biyo bayan tumbuke Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II da ofishin gwamnan jihar yayi.

Rundunar jami'an tsaron da suka hada da 'yan sanda da jami'an NSCDC ne suka mamaye harabar fadar, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Gwamnati ta jibge jami'an tsaro a fadar ne gabanin sanar da sabon sarkin da zai maye gurbin sarki Sanusi, kamar yadda jawabin gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana bayan sanar da tsige Sanusi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel