Mutuwa riga: Dan kwallon Najeriya ya mutu yayin da yake tsaka da taka leda

Mutuwa riga: Dan kwallon Najeriya ya mutu yayin da yake tsaka da taka leda

Dan kwallon Najeriya, Chineme Martins dake tsaron gida a kungiyar kwallon kafa ta Nassarawa United ya yanke jiki ya fadi, daga nan ya sheka barzahu a yayin da yake tsaka da taka leda.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito dan kwallon ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da kungiyarsa ta Nassarawa United ke karawa da kungiyar Katsina United, a filin wasa na Lafia dake jahar Nassarawa a ranar Lahadi, 8 ga watan Maris.

KU KARANTA: Majalisar dokokin jahar Kaduna ta yi dokar rage talauci a tsakanin talakawan Kaduna

Mutuwa riga: Dan kwallon Najeriya ya mutu yayin da yake tsaka da taka leda
Mutuwa riga: Dan kwallon Najeriya ya mutu yayin da yake tsaka da taka leda
Asali: Facebook

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Chineme ya yanke jiki ne a cikin fili bayan an dawo hutun rabin lokaci yayin da kungiyarsa Nassarawa United ke jan ragamar wasan da ci 2-0, koda ya fadi, an yi gaggawar garzayawa da shi zuwa asibitin Dalhatu Arab, inda a can aka tabbatar da mutuwarsa.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana cewa ya halarci kallon wasan a filin wasa dake Lafiya, ya kara da cewa: “Dan kwallon yana tsaye ne shi kadai a filin wasa jim kadan bayan dawo hutun rabin lokaci da misalin minti na 47.

“An baiwa kungiyarsa bugun tazara ne a lokacin, don haka yana tsaye a baya inda yake tsaron gida, kwatsam sai muka gan shi a kasa warwas, nan da nan aka sanar da Alkalin wasa, daga nan aka mika shi zuwa asibiti.” Inji shi.

Ita ma hukumar shirya gasar firimiya ta Najeriya, ta tabbatar da mutuwar Chineme, kuma ta yi alkawarin ganin an gudanar da bincike a kan gawarsa domin tabbatar da musabbabin mutuwar tasa.

“Muna fatan sakamakon binciken da za mu gudanar zai bamu haske game da matakin da ya kamata mu dauka a gaba idan har bamu da tsarin a yanzu.” Inji ta.

Haka zalika hukumar ta ce za ta cigaba da tuntubar kungiyar kwallon kafa ta Nassarawa United tare da iyalan mamacin don sanin hanyoyin da suka fi dacewa su basu tallafi da gudunmuwa a wannan lokaci da suke jimami da alhini.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng