Gwamnan jahar Imo, Hope Uzodinma, a ranar Lahadi, 8 ga watan Maris ya tsallake rijiya da baya lokacin da wasu matasa a yankin Ohaji Egbema da ke jahar suka far masa da hari.
A cewar jaridar Vanguard, a lokacin da wasu matasa suka hango motar Jeep na Uzodinma, sai suka fara yi masa ihun barawo, suna jifan motar da duwatsu.

Yanzun-nan: Fusatattun matasa a Imo sun kai wa Gwamna Hope Uzodinma hari, sun lalata masa mota
Source: UGC
Abubuwan da aka yi amfani dasu wajen jifan ya sa motar ya samu lahani, koda dai babu abun da ya samu gwamnan, tunda jami’ an tsaro sun tsere dashi.