Kakakin Osinbajo ya zayyana muhimman abubuwa 4 a kan maigidansa da jama'a basu sani ba

Kakakin Osinbajo ya zayyana muhimman abubuwa 4 a kan maigidansa da jama'a basu sani ba

Akwai a kalla wasu kyawawan halaye guda hudu da suka sa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya fita daban daga sauran shugabannin Najeriya, a cewar kakakinsa, Mista Laolu Akande.

Kakakin ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na taya Osinbajo murnar cika shekaru 63 a duniya.

Da yake yin karin bayani a kan kyawawan halayen Osinbajo, Akande ya bayyana cewa;

1. Osinbajo mutum ne mai matukar dogaro ga Allah, kuma hakan ne sirrin samun nasarorinsa a rayuwa.

2. Kaskan da kai da tawakkali ga Ubangiji su ne manyan makaman da Osinbajo ke amfani da su wajen samun nasara a kan duk abinda yasa a gaba.

Kakakin Osinbajo ya zayyana muhimman abubuwa 4 a kan maigidansa da jama'a basu sani ba

Osinbajo, Buhari da Akande
Source: Twitter

3. Aiki tukuru da kuma mayar da hankali a kan aiki sun kasance sirrin samun nasarorinsa a aiyukan da ya yi a baya da kuma wanda yake yi a yanzu.

DUBA WANNAN: NCC ta bayyana dalilin sake rufe wasu layukan waya miliyan 2.2

4. Ilimi da kuma yin abinda ya dace a lokacin da ya dace, musamman a al'amuran da suka shafi aikinsa da kuma mu'amala da jama'a.

Akande ya bayyana cewa wadannan kyawawan hali na Osinbajo ne suka sa shi ya baro Amurka domin yin aiki da gwamnatin Najeriya a karkashin mulkin Buhari/Osinbajo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel