Yanzu-yanzu: Lebura ya mutu yayin da ginin banki ya rufto masa a Legas

Yanzu-yanzu: Lebura ya mutu yayin da ginin banki ya rufto masa a Legas

Wani lebura ya mutu a daren ranar Asabar sakamakon rushewa da ginin Bankin Keystone da ke Palmgroove ya yi a Legas.

The Nation ta ruwaito cewa ana yi wa ginin benen da ke Ikorodu Road kwaskwarima ne a lokacin da ya rufto.

Lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 7.20 na yamma.

Yanzu-yanzu: Lebura ya mutu yayin da ginin banki ya rufto masa a Legas

Yanzu-yanzu: Lebura ya mutu yayin da ginin banki ya rufto masa a Legas
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Innalilahi: Bidiyon wani mutum da aka kama yana lalata da akuya a cikin kango

A lokacin rubuta wannan rahoton, jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Legas (LESEMA), Yan sanda da jami'an hukumar kula da gine-gine na jihar Legas (LABSCA) sun isa wurin.

Yanzu-yanzu: Lebura ya mutu yayin da ginin banki ya rufto masa a Legas

Yanzu-yanzu: Lebura ya mutu yayin da ginin banki ya rufto masa a Legas
Source: Twitter

Kazalika, jami'an hukumar kashe gobara sun isa wurin da abin ya faru domin dauke gawar mammacin tare da killace wurin.

Ku biyo mu domin samun cikakken rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel