Masu garkuwa da mutane sun cika hannu da tsohuwa yar shekara 80, uwar Ciyaman

Masu garkuwa da mutane sun cika hannu da tsohuwa yar shekara 80, uwar Ciyaman

Wasu miyagu marasa Imani sun tasa keyar wata tsohuwar mai shekaru 80 daga gidanta, inda suka yi awon gaba da ita tare da yin garkuwa da ita a yankin karamar hukumar Yenagoa na jahar Bayelsa.

Daily Trust ta ruwaito tsohuwar mai suna Madam Beauty Nimiyigha mahaifiya ce ga shugaban karamar hukumar Yenagoa, Mista Uropaye Nimiyigha, kuma yan bindigan sun sace ta ne da misalin karfe 11:40 na safe a gidanta dake Ekpetiama, Yenagoa.

KU KARANTA: Amincewa da bashin triliyan 8.2: Kun cuci yan Najeriya – PDP ga Sanatocin Najeriya

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa yan bindigan su biyar sun far ma yankin ne a cikin wata motar Nissan Pathfinder, inda suka yi ta harbin mai kan uwa da wabi wanda ya tsorata jama’an unguwar suka tsere, daga nan suka wuce da ita.

Yan bindigan sun yi tafiya mai tsawo da ita har zuwa gefen ruwa na yankin Amassoma, inda a can suka jefar da motar ta su, suka shige cikin wata kwale kwalen zamani mai inji dake jiransu, kafin a ankara sun bace a cikin ruwa.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Yansandan Najeriya reshen jahar Bayelsa, SP Asinim Butswat ya tabbatar da satar matar, inda yace tuni Yansanda sun kaddamar da farautarsu domin ceto madam Beauty.

A wani labarin kuma, wasu gungun miyagun yan bindigan daji sun yi garkuwa da kansiloli guda uku na karamar hukumar Gummi ta jahar Zamfara, kuma sun nemi a biyasu kimanin kudin fansa naira miliyan 40 kafin su sake su.

Kansilolin da aka yi garkuwan da su sun hada da Lawan Gummi, kansilar mazabar Ubandawaki, Murtala Arzika kansilan mazabar Gayari da Sahabi Abubakar kansilan mazabar Birnin Tudun Wada.

Majiyoyin sun bayyana cewa yan bindigan sun sace kansilolin ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Gusau daga karamar hukumar Gummi domin halartar wani taro. Haka zalika majiyoyi sun kara da cewa kansilolin basu dade da sauya sheka daga APC zuwa PDP ba.

Shugaban karamar hukumar Gumi, Alhaji Kabiru Aski ya bayyana guda daga cikin kansilolin, Murtala Arzika ya tsere daga hannun yan bindigan, yayin da miyagun ke cigaba da rike sauran guda biyun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng