Badakalar naira biliyan 2.2: Kotu ha haramtawa hukumar yaki da rashawa bibiyan Sarki Sunusi

Badakalar naira biliyan 2.2: Kotu ha haramtawa hukumar yaki da rashawa bibiyan Sarki Sunusi

Wata babbar kotun tarayya dake zamanta a jahar Kano ta dakatar da hukumar yaki da rashawa da karbar koke koken jama’a ta jahar Kano daga cigaban da binciken mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II.

Daily Trust ta ruwaito Sarki Sunusi II ya shigar da karar hukumar gaban kotun inda ya roketa ta baiwa hukumar umarnin dakatar da duk wani bincike da take yi a kansa dangane da bahallatsar cin filaye da darajarsu ta kai naira biliyan 2.2.

KU KARANTA: Amincewa da bashin triliyan 8.2: Kun cuci yan Najeriya – PDP ga Sanatocin Najeriya

Baya ga hukumar, sauran wadanda Sarkin ya maka a gaban kotun sun hada gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, shugaban hukumar yaki da rashawa da karbar koke koken jama’a ta jahar Kano, Muhyi Magaji Rimingado, da kuma babban lauyan jahar Kano, Ibrahim Mukhtar.

A ranar Alhamis ne hukumar yaki da rashawa da karbar koke koken jama’a ta jahar Kano ta tabbatar da manufarta na binciken Sarkin Kano game da zargin da ake masa na sayar da wasu kadarorin masarautar Kano.

Shugaban hukumar, Muhyi Mahaji ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labaru inda yace tuni hukumar ta mika ma Sarki takardar gayyata don ya gurfana a gabanta domin amsa tambayoyi a ranar Litinin, 9 ga watan Maris da misalin karfe 10 na safe.

Sai dai lauyoyin Sarki, Dikko & Mahmoud sun nemi kotu ta dakatar da hukumar daga cigaba da gudanar da wannan bincike, haka kuwa aka yi, inda Alkalin kotun, mai sharia Lewis Allagoa ya umarci hukumar ta dakata da bincikenta har sai an kammala sharia’ar dake gabanta.

Daga nan Alkalin ya dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2020. Shi ma a nasa jawabin, shugaban hukumar, Muhyi Magaji ya ce zasu yi ma kotun biyayya ta hanyar bayyana a gabanta a ranar 18 ga watan Maris.

Muhyi ya kara da cewa: “Za mu bukaci kotu ta tilasta ma Sarki bayyana a gaban hukumar domin hukuncin kotun bai hana cigaba da gudanar da bincike a kan sa ba.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel