Sarkin Saudiyya ya sallami manyan ministocinsa, ya sauya wa wasu ma'aikata

Sarkin Saudiyya ya sallami manyan ministocinsa, ya sauya wa wasu ma'aikata

- Sarki Salman na kasar Saudi Arabia ya sallami ministan tattalin arziki a girgizar da yayi da sauyawa shugabannin wajen aiki

- Hakan kuwa ta faru ne sakamakon faduwar farashin man fetur kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaran kasar Saudi din ya ce

- Sarkin ya hori ministan kudin kasar, Mohammed al-Jaadan da ya karba ragamar ma'aikatar

Sarki Salman na kasar Saudi Arabia ya sallami ministan tattalin arziki a girgizar da yayi da sauyawa shugabannin wajen aiki, kafar yada labaran gwamnatin kasar ta ruwaito.

Hakan kuwa ta faru ne sakamakon faduwar farashin man fetur. Kamfanin Dillancin Labaran kasar Saudi din ya ce, Sarkin ya sauwakewa Mohammed al-Tuwaijiri matsayinsa na ministan man fetur kuma ya hori ministan kudin kasar, Mohammed al-Jaadan da ya karba ragamar ma'aikatar.

Tuwaijiri dai an zabesa a matsayin mai bayar da shawara ne ga kotun masarautar a matsayin minista, kamfanin dillancin labaran kasar ya sanar.

Wannan ya faru ne bayan kwanaki 10 da kasar Saudi Arabia din ta sanar da kirkiro sabbin ma'aikatu uku na bude ido, wasanni da saka hannun jari.

Sarkin Saudiyya ya sallami manyan ministocinsa, ya sauya wa wasu ma'aikata

Sarkin Saudiyya ya sallami manyan ministocinsa, ya sauya wa wasu ma'aikata
Source: Getty Images

DUBA WANNAN: Za a fara biyan 'yan N-Power allawus din Janairu da Fabrairu ranar Juma'a - FG

Girgiza mulkin kasar a watan da ya gabata yasa dawowar tsohon ministan wutar lantarki, Khalid al-Falih zuwa fagen siyasa a matsayin ministan saka hannayen jari.

An sallami Falih ne daga ma'aikatar wutar lantarki a girgizar da aka yi a watan Satumba da ta gabata kuma Yarima Abdulaziz bin Salman ya maye gurbinsa.

Wannan sauye-sauyen sun zo ne a yayin da kasar Saudi Arabia din ke fama da kankantar farashin wutar lantarki kuma take neman hanyar samuwar aiyuka a bangarorin da ba na man fetur ba da suka hada da yawon bude ido, wasanni da kuma nishadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel