Amincewa da bashin triliyan 8.2: Kun cuci yan Najeriya – PDP ga Sanatocin Najeriya

Amincewa da bashin triliyan 8.2: Kun cuci yan Najeriya – PDP ga Sanatocin Najeriya

Jam’iyyar PDP ta ga baiken sanatocin Najeriya da suka amince da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari na ciyo ma Najeriya bashin dala biliyan 22.7, kimanin naira tiriliyan 8.2 kenan, inda suka ce Sanatocin sun kara ma yan Najeriya wahala.

Daily Trust ta ruwaito PDP ta bayyana haka ne ta bakin sakataren watsa labarunta, Kola Ologbandiyan, wanda ya daura laifin kacokan ga Sanatocin jam’iyyar APC, ya kara da cewa abin haushin shi ne yadda Sanatocin suka amince da bashin ba tare da gwamatin ta bayar da gamsashshen bayanin yadda za ta kashe su ba.

KU KARANTA: Coronavirus: Masarautar Saudiyya ta bude Masallatan Makkah da Madina bayan tsaftace su

“Duba da yadda APC ke neman ciyo ma yan Najeriya bashin zambar kudi dala biliyan 22.7 wanda daga ciki har da dala miliyan 500 da sunan gyaran hukumar gidan talabijin na NTA ya nuna APC, da shafaffu da main a fadar shugaban kasa sun kitsa wata almundahana.

“Wannan yasa basu dama su jefa yan Najeriya cikin mawuyacin hali don biyan bukatarsu ba. Su ma Sanatocin APC da suka amince da wannan bukata duk da sanin yan Najeriya basu goyon bayan hakan, sun nuna bakin su daya da sauran shuwagabannin APC don sace kudin kasa tare da cutar da yan Najeriya.

“Jam’iyyar ta damu kwarai game da yadda gwamnatin shugaban kasa Buhari ke tula ma Najeriya basussuka ba tare da wani takamaimen abin da suka yi da kudin ba, illa wahalar rashin aiki da tabarbarewar ababen more rayuwa, ga kuma matsalar tsaro dsa talauci.

“Muna kara jinjina ma Sanatocinmu na PDP bisa yadda suka tsaya tsayin daka ta hanyar fatali da bashin kudin don ganin ba’a cutar da yan Najeriya ba.”Inji shi.

A ranar Alhamis ne majalisar dattawa ta amince ma Buhari ya ciyo bashin dala biliyan 22.7 bayan wata ganawar gaggawa da yayan majalisar suka yi, sai dai an yi takaddama kafin samun amincewar majalisar.

Takaddamar da ta samo asali ne lokacin da shugaban kwamitin kula da basussukan gwamnati na ciki da wajen kasar nan, Sanata Clifford Odia ya mika ma majalisa rahotonsa, daga nan Sanatan PDP Abaribe ya nemi a bayyana ayyukan da gwamnatin tarayya da ta aiwatar da kudaden.

Abaribe ya nemi kwamitin ta bayyana ma majalisa ayyukan da za’a gudanar da kudaden ne domin yan majalisa su tattauna muhimmancin ayyukan tare da auna amfaninsu ga jama’a ko akasin haka.

Hakan ya haifar da cacar baki a tsakanin yan majalisar da har ya tilasta su shiga ganawar sirri, daga bisani bayan daukan kimanin mintuna ashirin suna tataunawa sai majalisar ta sanar da amincewarta da amso bashin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel