Yan bindiga sun cika hannu da kansiloli 3 a jahar Zamfara, sun nemi naira miliyan 40

Yan bindiga sun cika hannu da kansiloli 3 a jahar Zamfara, sun nemi naira miliyan 40

Wasu gungun miyagun yan bindigan daji sun yi garkuwa da kansiloli guda uku na karamar hukumar Gummi ta jahar Zamfara, kuma sun nemi a biyasu kimanin kudin fansa naira miliyan 40 kafin su sake su.

Jaridar Punch ta ruwaito kansilolin da aka yi garkuwan da su sun hada da Lawan Gummi, kansilar mazabar Ubandawaki, Murtala Arzika kansilan mazabar Gayari da Sahabi Abubakar kansilan mazabar Birnin Tudun Wada.

KU KARANTA: Coronavirus: Masarautar Saudiyya ta bude Masallatan Makkah da Madina bayan tsaftace su

Majiyoyin sun bayyana cewa yan bindigan sun sace kansilolin ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Gusau daga karamar hukumar Gummi domin halartar wani taro. Haka zalika majiyoyi sun kara da cewa kansilolin basu dade da sauya sheka daga APC zuwa PDP ba.

Shugaban karamar hukumar Gumi, Alhaji Kabiru Aski ya bayyana guda daga cikin kansilolin, Murtala Arzika ya tsere daga hannun yan bindigan, yayin da miyagun ke cigaba da rike sauran guda biyun.

Daga karshe Ciyaman Aski ya bayyana cewa karamar hukumar na cigaba da kokarin an sako sauran mutanen biyu.

A wani labarin kuma, bangaren dakarun rundunar Sojan sama na Operation Lafiya Dole sun cigaba da yi ma mayakan kungiyar yan ta’addan kungiyar Boko Haram ruwan wuta da bama bamai a yankin Bakari Gana dake gefen dajin Sambisa.

Daraktan watsa labaru na rundunar Sojan sama, Ibikunle Daramola ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 5 ga watan Maris, inda ya ce sun kai hare haren ne a ranar Laraba a jahar Borno.

Daramola ya kara da cewa an kirkiri Operation Decisive Edge ne don lalubo duk inda mafakar ko mabuyar yan Boko Haram take tare da ragargazarsa, musamman inda Sojoji ba za su iya shigar a kafa ba saboda yanayin lungun ko kuma sun zagaye shi da bamabaman da suka binne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel