Damfara: An gurfanar da Mama Boko Haram gaban alƙali na uku
- Hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta gurfanar da Aisha Wakil wacce aka fi sani da Mama Boko Haram
- Wannan ne karo na uku dai da aka gurfanar da ita tare da wasu mutane biyu a kan laifuka takwas da ake zarginsu da shi da ya hada da damfara
- Da farkon makon nan ne dai aka gurfanar da mutane ukun da karin wani mutum daya a gaban Mai shari’a Aisha Kumaliya ta babban kotun jihar Borno
Hukumar yaki da rashawa ta EFCC a ranar Alhamis ta gurfanar da Aisha Wakil, wacce aka fi sani da Mama Boko Haram, tare da wasu mutane biyu a kan zarginsu da take da laifuka 8 da suka hada da damfara.
Wannan ne yasa aka gurfanar da ita da sauran wadanda ake zargin a kan damfara a gaban alkalai uku na jihar.
Sauran biyun da ake zargi tare da ita din sun gurfana ne a gaban Mai shari’a Umaru Fadawu na babban kotun jihar Borno da ke Maiduguri. Sun hada da babban dan wata kungiyar taimakon kai da kai mai suna Complete Care anda Aid Foundation, Alhaji Saidu Daura da kuma Prince Lawal Shoyode.
Da farkon makon nan ne dai aka gurfanar da mutane ukun da karin wani mutum daya a gaban Mai shari’a Aisha Kumaliya ta babban kotun jihar Borno, a kan damfarar makuden kudade har N111.7m.
DUBA WANNAN: Bidiyon dan sanda da ya daka tsalle ya dare kan motar da ke gudu a titi don ya tsayar da direban
Wakil da Daura na fuskantar zargin rashawa ne ta naira miliyan 66 a gaban mai shari’a Aisha Kumaliya.
A farkon shekarar nan ne Wakil, Daura, Shoyode da Mallam Adamu Sani aka gurfanar da su a kan damfara naira miliyan 42 a gaban Mai shari’a Dagat ta babbar kotun tarayya da ke Maiduguri.
A yayin da Wakil ta musanta duk zargin da ake mata a ranar Alhamis, sauran mutane biyun basu musanta ba.
Bayan hakan ne lauyar EFCC din mai suna Fatsuma Muhammad ta bukaci a saka wata rana don masu korafin su kawo shaidunsu a kan wadanda ake zargin.
Mai shari’a Fadawu ta dage sauraron karar zuwa ranar 12 da kuma 16 ga watan Maris na 2020.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng