Bidiyo: Baturiya ta kama aikin tukin motar haya don ta samu na kashewa a kasar Ghana

Bidiyo: Baturiya ta kama aikin tukin motar haya don ta samu na kashewa a kasar Ghana

- Bidiyon wata Baturiya dake ta faman yawo a kafafen sadarwa ya jawo kace-nace matuka

- Bidiyon wanda ya nuna wata Baturiya tana sana'ar hayar mota a kasar Ghana ya sanya mutane sun cika da mamaki

- Da yawa daga cikin mutane sun bayyana cewa tana yin wannan aikine saboda ta samu na sayen abinci da sauransu

Idan har kana tunanin tuka motar haya aikine na mutane marasa ilimi sosai da kuma mutane marasa daraja, to kwarai kuwa zaka sha mamaki idan har bakin haure suka kwace aikin daga hannun 'yan gari.

Wani bidiyo da yake ta faman yawo a kafafen sadarwa ya nuna wata mata Baturiya mai dan matsakaicin shekaru tana tuka motar haya domin ta samu kudin da za ta rayu ba tare da matsala ba.

Bidiyon wanda wani mai suna Dr. Ayigbe Borla ya wallafa, ya jawo kace-nace matuka a kafafen sadarwa idan da yawa suke yabawa Baturiyar akan wannan abu da take yi ba tare da takurawa rayuwarta ba.

Sai dai mutane kowa na ta fadar abinda yake ransa ne, inda wasu ke cewa Baturiyar na amfani da motar domin ta samu na kashewa ne, wasu kuma sun ce tana amfani da motar wajen ayyukanta na yau da kullu ne.

KU KARANTA: Mutumin da ya nemi aiki sau 200 bai samu ba yanzu yana samun sama da naira miliyan hudu duk wata

To dama dai kowa ya san su Turawa basu da raina sana'a duk kankantar ta, mutanen nahiyar Afrika ne suke da son sai sun yi sana'ar da idan kowa ya gan su zai san cewa suna sana'a mai kyau.

Hakan ba karamin kalubale bane ga al'ummar yankin domin kuwa rashin sana'a na daya daga cikin muhimman abubuwan da suke kara kawo bakin talauci a nahiyar ta Afrika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel