Oshiomole ya bayyana babban dalilin da yasa makiyansa ke kokarin cire daga shugabantar APC

Oshiomole ya bayyana babban dalilin da yasa makiyansa ke kokarin cire daga shugabantar APC

Shugaban jam’iyyar APC ta kasa, Kwamared Adams Oshiomole ya bayyana dalilin da yasa wasu yayan jam’iyyar APC wadanda yake kallonsu a matsayin makiyansa suke kokarin tsige shi daga kujerar shugabancin jam’iyyar.

Daily Trust ta ruwaito Oshiomole ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru jim kadan bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnatin Najeriya a ranar Alhamis.

KU KARANTA: EFCC da ICPC za su fara kama matasan N-Power dake cin albashi amma basa aiki

Wannan jawabi na Oshiomole ya zo ne jim kadan bayan wata babbar kotun tarayya dake zamanta a jahar Kano ta soke dakatarwar da wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja ta yi masa a ranar Laraba.

A cewarsa, ya kai ziyarar ne domin bayyana ma shugaban kasa halin da ake ciki a tirka tirkar da ta dabaibaye jam’iyyar APC, sa’annan yace akwai wani minista a gwamnatin Buhari da wasu gwamnoni dake shirya masa duk wani tuggu.

Sai dai Oshimole ya bayyana cewa duk masu son ganin bayansa a jam’iyyar APC suna yi ne kawai don suna son zama shugaban kasar Najeriya a zaben shekarar 2023, amma kuma basu da iko da jam’iyyar a jahohinsu.

A wani labarin kuma, Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, kuma gwamnan jahar Ekiti, John Kayode Fayemi ya warware zare da abawa game da batun tsayawarsa takarar shugabancin kasar nan a zaben shekarar 2023.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne ta bakin mai magana da yawunsa, Segun Dipe, inda ya bayyana cewa ba shi da wani burin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.

Don haka gwamnan yace masu yada wannan jita jita a kansa suna yi ne ba tare da sani ko amincewar sa ba. Mista Dipe ya bayyana cewa duk masu yayata batun basu san Gwamna Fayemi ba, kuma basu san alakarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar Dipe, duk da cewa Fayemi ya cika dukkanin shika shikan tsayawa takarar shugaban kasa daga yankin kudu maso yammacin Najeriya, amma ya fi son ya cigaba da jan ragamar kungiyar gwamnonin Najeriya tare da kokarin hada kawunan gwamnanonin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng