Kananan Sojoji sun kai ma Buhari kuka bisa yadda wani babban Soja yake cinye hakkokinsu

Kananan Sojoji sun kai ma Buhari kuka bisa yadda wani babban Soja yake cinye hakkokinsu

Wasu dakarun Sojojin Najeriya dake yaki da kungiyar Boko Haram a jahar Borno sun aika ma sakon koke ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai game da wani babban Soja dake cinye hakkokinsu.

Jaridar The Nation ta ruwaito Sojojin sun bayyana cewa babban Sojan yana cinye hakkokinsu da alawus alawus, kuma ya ki biyansu sabon alawus N200 na kudin sigari da rundunar Sojan kasa ta fara biya tun a watan Janairu.

KU KARANTA: Artabun Sojoji da Boko Haram a Damboa: Gwamna Zulum ya yaba da jarumtar zaratan Sojojin Najeriya

Sojojin sun ce a maimakon alawus din kudin walwala na N24,000, wanda ya hada da N12,000 da babban hafsan Soja yake biyansu, amma sai kwamandan nasu yake biyansu N12,000 kacal, amma sauran kwamandojin bataliya suna biyan Sojojin bataliyars N24,000.

Haka zalika sun koka kan cewa ya daina tura mota da yan rakiya zuwa Maiduguri da zasu dauko Sojojin da suka dawo daga hutu, ba kamar yadda kwamandojin baya suke yi ba.

“Babu ruwansa da yadda Sojoji suke shiga motocin fararen hula idan zasu koma sansaninsu, kuma duk wanda bai koma ba sai ya cire masa N800 daga albashinsa, tun ma kafin karin alawus, tsofaffin kwamandojinmu suna bamu kwalin siga, leda 12 na Chocolate, kwai 12, amma bayan nada Laftanar Kanal Asemota sai ya daina, wai baya so ya ga muna kyau.

“Ya daina bamu daman fita zuwa gari, sai ka yi watanni 7 zuwa 8 kafin ka samu wannan dama, don haka muke kira gareka ka duba wannan matsalar ta mu da idon basira domin mu samu karin kuzarin yaki da yan ta’adda.” Inji koken.

Sai dai mai magana da yawun Operation Lafiya Dole, Kanal Aminu Iliyasu ya bayyana cewa akwai hanyar da ake bi wajen kai koke a gidan Soja, don haka Sojojin nan sun karya doka, amma duk da haka yace zasu kafa kwamitin bincike don gano gaskiyar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel