EFCC da ICPC za su fara kama matasan N-Power dake cin albashi amma basa aiki

EFCC da ICPC za su fara kama matasan N-Power dake cin albashi amma basa aiki

Babban hadimin shugaban kasa a kan sha’anin samar ma matasa aikin yi, Afolabi Imoukhuede ya bayyana cewa mahukunta shirin tallafin gwamnatin tarayya na N-Power za su hada kai da hukumomin yaki da rashawa don kama matasan dake cin gajiyar N-Power amma basa zuwa aiki.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Afolabi ya bayyana haka ne yayin da bayyana bacin ransa game da yadda ake samun karin matasan N-Power da basa zuwa wajen aikin da aka tura su, kuma suna cin albashi a bagas.

KU KARANTA: Artabun Sojoji da Boko Haram a Damboa: Gwamna Zulum ya yaba da jarumtar zaratan Sojojin Najeriya

“Muna samun korafe korafe a kan ma’aikatan N-Power da basa zuwa wajen aiki, kuma koken na karuwa, amma ina tabbatar maka muna da tsarin bin diddigi a karkashin N-Power, musamman game da wadanda suke tafiya ba tare da samun izini ba.

“Don haka akwai hukuncin mai tsauri ga duk wadanda suke ganin za su iya tafiyarsu a duk lokacin da suka ga dama.” Inji shi.

Ya kara da cewa duk wanda ya gaji da aikin N-Power yana da daman ajiye aikin a maimakon ya ki zuwa wajen aiki kuma yana karbar albashi, akwai mutane 5,781 da aka cire daga tsarin sabon rashin zuwa wajen aiki.

“Mun samu mutane 11,238 da suka nuna sha’awarsu na ajiye aiki, mun amince da cire mutane 8,709 daga cikinsu saboda sun bi duk tsare tsaren da ake bi, kuma sun tabbatar mana da sha’awarsu, amma mutane 2,529 suna jira har yanzu saboda mun kasa samunsu a lambobin wayar tarho da suka daura a shafin yanar gizo na N-Power, domin mu tabbatar daga bakinsu.

“A karkashin tsarin N-Power, kana koyon aiki, kuma ka yi aiki, sa’annan a biyaka, amma idan baka yi aiki ba aka biyaka, toh ba ka ci halas ba, satar kudin al’ummar kasa ka yi, kasar da ta yi maka alheri.” Inji shi.

Daga karshe ya yi kira ga masu sha’awar barin aikin su yi murabus, saboda hakan ya bayyana su a matsayin yan kasa nagari, kuma zai baiwa wasu yan Najeriya daman cin gajiyar tsarin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel