Shirin aure ya watse bayan an gano saurayi da budurwa 'yan uwa ne

Shirin aure ya watse bayan an gano saurayi da budurwa 'yan uwa ne

- Wasu masoya biyu ‘yan asalin kasar Kenya wadanda suka dade suna cin soyayyarsu, sun gano cewa su ‘yan uwa juna ne

- An umarci John Njoroge da ya tsayar da shirye-shiryen aurensu da Rose Wanjiku saboda ‘yan uwan juna ne

- A yayin tuna wa da mummunan lamarin da ya tsinci kan shi, Njorege ya ce an sanar da shi cewa Wanjiku ‘yar uwar shi ce don ‘yar matar mahaifin shi

Wasu masoya biyu ‘yan asalin kasar Kenya wadanda suka dade suna cin soyayyarsu, sun gano cewa su ‘yan uwa juna ne yayin da ake sauran kwanaki kadan bikinsu.

An umarci John Njoroge da ya tsayar da shirye-shiryen aurensu da Rose Wanjiku saboda ‘yan uwan juna ne.. An kuwa gano hakan ne bayan gaisuwar iyaye da aka je yi.

Shirin aure ya watse bayan an gano saurayi da budurwa 'yan uwa ne

Shirin aure ya watse bayan an gano saurayi da budurwa 'yan uwa ne
Source: Twitter

A yayin tuna wa da mummunan lamarin da ya tsinci kan shi, Njorege ya ce an sanar da shi cewa Wanjiku ‘yar uwar shi ce don ‘yar matar mahaifin shi ta biyu ne.

DUBA WANNAN: IGP ya bayyana su waye 'yan bindigan yankin Arewa maso Yamma

Ya sanar da gidan talabijin din Kameme cewa: “Bayan na kai ta wajen iyayena don gabatarwa, an sanar da ni cewa mahaifina yana da wata mata kuma wannan ‘yar ta ce. Wannan na nuna cewa ‘yar uwata ce ta jini.”

Shirin aure ya watse bayan an gano saurayi da budurwa 'yan uwa ne

Shirin aure ya watse bayan an gano saurayi da budurwa 'yan uwa ne
Source: UGC

Njiroge wanda ya fara soyayya da budurwar bayan ta siya takalmi daga wajen shi, ya ce sun fara soyayya ne kuma sun fahimci juna ba kadan ba.

A bangarenta, Wanjiku ta bayyana yadda take tsoron fadawa soyayyar wani. Ta ce: “Ba zan iya fara soyayya da wani mutum ba saboda ina tsoron kada ya zamo daga cikin ‘yan uwana ne.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel