Yanzu-yanzu: Minista da wasu gwamnoni suka shirya tuggun dakatad da ni - Oshiomole bayan ganawarsa da Buhari

Yanzu-yanzu: Minista da wasu gwamnoni suka shirya tuggun dakatad da ni - Oshiomole bayan ganawarsa da Buhari

Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya bayyana cewa wani ministan Buhari da wasu gwamnoni ne suka shirya masa tuggun tsigeshi ta hanyar kotu.

Ya bayyana hakan ne ga manema labaran fadar shugaban kasa bayan ganawar da yayi da shugaba Muhammadu Buhari a Aso Rock a yau.

Oshiomole ya sifanta kansa a matsayin hasken ranan da ya bayyana kuma babu wani tafin hannu da zai iya karewa.

Amma ya ki ambatan sunayen Ministan da gwamnonin.

Yanzu-yanzu: Minista da wasu gwamnoni suka shirya tuggun dakatad da ni - Oshiomole bayan ganawarsa da Buhari

Oshiomole bayan ganawarsa da Buhari
Source: Twitter

Mun kawo muku rahoton cewa Sakamakon dakatad da shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa, Adams Oshiomole, a ranar Laraba da kotu tayi, hukumar yan sanda ta garkame hedkwatan jam'iyyar dake Blantyre Street, unguwar Wuse 2, Abuja.

Da safiyar yau Alhamis, jami'an yan sanda akalla hamsin sun yiwa hedkwatar da titin gaba daya zobe. A cewar majiya mai sika, kwamishanan yan sandan birnin tarayya da mataimakansa guda biyu sun dira ofishin da safen nan.

Majiyar ta ce an tura jami'an yan sanda hedkwatar ne saboda labarin da aka samu cewa dakataccen shugaban jam'iyyar, Adams Oshiomole, na shirin zuwa ofishin.

Wani jami'in tsaro a hedkwatar APC ya bayyanaw manema labarai cewa yan sandan na samun labarin cewa Oshiomole na shirin zuwa aka turo jami'ai da yawa.

Ya ce kwamishanan yan sandan ya bada umurnin cewa kada a sake a bari kowa ya shiga cikin sakatariyan har sai wani mamban kwamitin gudanarwa jam'iyyar ya zo wajen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel