Yanzu-yanzu: An haramta bara a jihar Neja

Yanzu-yanzu: An haramta bara a jihar Neja

Gwamnatin jihar Neja karkashin jagoraninc gwamna Abubakar Sani Bello, ta haramta kowani irin bara a titi a fadin jihar saboda dalilai na tsaro.

Kwamishanan yada labaran jihar, Mohammed Idris, ya bayyana hakan ne a hira da yayi da manema labarai a Minna, inda yace abinda majalisar zantarwar jihar ta zartar kenan a ganawarta na mako-mako.

Ya ce wannan doka za ta fara aiki ne daga ranar 5 ga Maris, saboda rahotanni daga hukumomin tsaro ya tilastawa gwamnatin jihar daukan mataki mai tsauri kan bara da mabarata.

“An yi hakan ne saboda akwai lamarin rashin tsaro dake karuwa kullun a jihar, saboda haka haramta bara zai taimaka wajen rage wadannan kalubale.,” Yace

Idris ya ce an dau wannan mataki ne domin kare rayuka da dukiyan mazauna jihar kuma za a tsaurara matakai kan wadannan sukayi kunnen kashi.

Ya kara da cewa, za a damke duk wani babba da aka kama yana bara, kuma a hukunta iyayen yaran da aka kama suna bara a titi.

Yanzu-yanzu: An haramta bara a jihar Neja

Yanzu-yanzu: An haramta bara a jihar Neja
Source: Depositphotos

KU KARANTA Yanzu-yanzu: Majalisar dattawa ta baiwa Buhari daman karbo bashin $23bn

Shahrarren masanin addinin Islama, Dakta Mansur Ibrahim Sokoto, ya yabawa gwamnatocin jihar Kano da Nasarawa kan haramta bara ga Almajirai.

Malamin ya bayyana cewa can dama babu wata alaka tsakanin bara da almajiranci. ya yi kira ga gwamnonin sun fito da wasu hanyoyin rage talauci da yunwa cikin masu aikin barace-barace.

A cewarsa: “Bara daban, almajirci daban. Matakin da jihohin Kano da Nasarawa suka dauka abin yabawa ne, da sharadin a fito da karfafan hanyoyin rage radadin talauci.“

Mun kawo muku rahoton cewa gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya haramta bara a titunan jihar.

Ya sanar da hakan ne yayin rantsar da hukumar kare hakkin yara a Lafia a ranar Laraba.

Hakazalika gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Talata ya alanta dokar haramta bara ga almajirai a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel