Shugabannin da suka saci kudin al'umma sune suka fi kowa talauci a gaban Allah - Sheikh Awal

Shugabannin da suka saci kudin al'umma sune suka fi kowa talauci a gaban Allah - Sheikh Awal

- Masu mulki da ke azurta kan su ta hanyar handame kudin jama’a sune suka fi kowa fatara a wajen Allah

- Sheikh Awal ya sanar da hakan ne ga Kamfanin Dillancin Labaran kasar Ghana bayan jan sallar Juma’a a jami’ar kimiyya da fasaha da ke Kwame

- Sheikh Awal ya ce abin haushi ne da takaici idan aka dubi yawwancin shugabannin nahiyar Afrika yadda suke mulki

Masu mulki da ke azurta kan su ta hanyar handame kudin jama’a sune suka fi kowa fatara a wajen Allah, sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Mohammed Awal ya sanar.

Ya ce mutane zasu iya zama masu arziki a cikin jama’a, amma su ba komai bane a wajen Allah mai girma da buwaya, saboda hanyoyin da suka bi wajen tara dukiyar.

Ya ce ba a amincewa mutanen da aka ba shugabanci ba tattara dukiyar al’umma don amfanin kansu ko azurta kansu ba.

Sheikh Awal ya sanar da hakan ne ga Kamfanin Dillancin Labaran kasar Ghana bayan jan sallar Juma’a a jami’ar kimiyya da fasaha da ke Kwame Nkrumah da yayi.

Ya ce babu dacewa a ce a zabi mutum don wakilci amma ya kare da zurta kan shi. Ya ce duk wanda ya nemi mulki don azurta kan shi da kudin haram ba zai samu wata nasarar ba saboda sun rasa goyon bayan jama’a da na Ubangiji.

KU KARANTA: Na cika da mamaki dana ga sunana cikin fitattun mutane a Kano - Nazifi Asnanic

Sheikh Awal ya ce abin haushi ne da takaici idan aka dubi yawancin shugabannin nahiyar Afrika. A maimakon samar da al’umma ta gari da wakilcin da ya dace, su kan talauta kasa ne tare da ikirarin cewa suna aiki ne saboda jama’a.

“Abinda ke faruwa a yanzu shine yadda talakawa ke shan wahala yayin da masu mulki ke morewa. Amma wannan bai dace a ce yana faruwa ba a tsarin mulkin damokaradiyya da kuma gwamnatin jama’a,” yace.

Malamin addinin Musuluncin mazaunin Amurka ne kuma ya tunatar da shugabanni a Afrika a kan hisabi da ranar sakamako.

Ya jaddada bukatar amfani da abinda akwai don samar da rayuwa mai kyau ga jama’a tare da habaka su ta yadda ba zasu dogara da kowa ba.

Dole ne su dau lokaci mai kyau don gyara rayuwar matasa sannan su koya musu dabarun mulki, Sheikh Awal yace.

“Wannan zai yuwu ne bayan an cusawa matasan kishin kasa tare da koya musu dabarun mulki a matsayinsu na manyan gobe a fadin duniya.” Ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel