Artabun Sojoji da Boko Haram a Damboa: Gwamna Zulum ya yaba da jarumtar zaratan Sojojin Najeriya

Artabun Sojoji da Boko Haram a Damboa: Gwamna Zulum ya yaba da jarumtar zaratan Sojojin Najeriya

Gwamnan jahar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya jinjina tare da yaba ma dakarun Sojojin Najeriya na Operation lafiya Dole bisa jarumtar da suka nuna a yayin artabun da suka yi mayakan Boko Haram a Damboa a ranar Laraba.

Zulum ya bayyana haka ne a shafinsa na Facebook, inda yace ba zai iya jurewa ba har sai ya bayyana ma duniya yadda Sojojin Najeriya na sama da na kasa suka yi ma yan Boko Haram rakiyar kura tare da tafka musu mummunan asara.

KU KARANTA: Miyagun yan bindiga su 15 sun tarwatsa yan kasuwa a jahar Zamfara

Artabun Sojoji da Boko Haram a Damboa: Gwamna Zulum ya yaba da jarumtar zaratan Sojojin Najeriya

Artabun Sojoji da Boko Haram a Damboa: Gwamna Zulum ya yaba da jarumtar zaratan Sojojin Najeriya
Source: Facebook

“Da misalin karfe 6 na safiyar Laraba yan Boko Haram suka kaddamar da hari a garin Damboa ta bangarori daban daban da nufin afka ma garin, sai dai sun ci karo da zaratan Sojoji dake cikin shirin yaki a kullum, nan da dakarun kasa da na sama suka shiga artabu dasu.

“A hannu guda Sojojin sa kai na Civilian JTF da yan banga suna taimaka musu, nan take suka lalata motocin Boko Haram 13, tare da kashe duk wadanda suke ciki. Amma abin da ya fi burgeni shi ne bayan yan ta’addan sun tsere, Sojoji basu tsaya ba, sai suka bi su a guje har sai da suka sake lalata motocinsu guda 6, tare da kashe karin yan ta’adda da dama.

“Hakan ya kawo adadin motocin da Sojoji suka lalata ma Boko Haram zuwa 19 a artabun, mun san muhimmancin mota daya a hannun Boko Haram, balle kuma motoci 19. Don haka nake jinjina ma matasa yan sa kai da suka taimaka ma Sojoji.

“Ina jinjina ma matasan sa kai biyu da suka mutu a kokarinsu na kare jahar Borno da Najeriya, ina jajanta ma iyalan wasu mata biyu da suka mutu a sanadiyyar harsashi da ya same su a yayin artabun, sa’annan ina fatan Allah Ya baiwa wadanda suka jikkata sauki.” Inji shi.

Daga karshe gwamnan ya jaddada yakininsa na samun nasara a kan yan ta’addan tare da dawowar zaman lafiya mai daurewa, da ikon Allah.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel