Miyagun yan bindiga su 15 sun tarwatsa yan kasuwa a jahar Zamfara

Miyagun yan bindiga su 15 sun tarwatsa yan kasuwa a jahar Zamfara

Wasu gungun miyagun yan bindiga sun kai mummunan hari a wata kasuwar kauye mai suna kasuwar Mutunji dake cikin garin Dan Sadau na karamar hukumar Maru a jahar Zamfara, inda suka yi harbe harbe tare da kwace kudaden jama’a.

BBC Hausa ta ruwaito yan bindigan da yawansu ya kai 15 sun kai harin ne da tsakar ranar Laraba, 5 ga watan Maris a kan babura, inda shigarsu ke da wuya suka fara harbe harben mai kan uwa da wabi.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Nassarawa za ta kwashe almajirai 63,000 zuwa jahohinsu na asali

Jami’in hulda da jama’a na rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Zamfara, SP Muhammad Shehu ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa da ba don isar jami’an Yansanda zuwa kasuwar a yayin da yan bindigan suka kai harin ba da barnar da za sy tafka ya wuce haka.

Ita dai wannan kasuwa ta shahara wajen sayar da kayan lambu da dabbobi, amma ta dade a rufe sakamakon hare haren yan bindiga da ya addabi yankin Dan Sadau da Maru, duka duka bai wuce watanni biyu da budeta ba.

Wani shaidan gani da ido ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa yan bindigan sun kwace kudaden jama’a, kuma sun kwashi lemo da ruwan sanyi daga shagon wani mutumi, sa’annan suka kara wuta.

A wani labari kuma, Wasu gungun yan bindiga sun bude ma jama’a wuta a mahadar hanyar Ekete cikin karamar hukumar Udu na jahar Delta, inda suka kashe jami’an Yansanda guda biyu da wani farar hula guda daya.

Yan bindigan sun kai harin ne a daren Talata, 3 ga watan Maris, inda suka kashe yansandan dake tsaron Club 316 ne, sa’annan suka bindige wani farar hula guda daya, tare da kwashe makamansu.

A hannu guda kuma, kwamishinan Yansandan jahar Delta, Hafiz Inuwa ya sanar da kama wasu miyagun mutane masu sata tare da garkuwa da jama’an da basu ji ba, basu gani ba a yankin Sapele na jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng