Shugaban gwamnonin Najeriya ya yi magana game da takarar shugaban kasa a 2023

Shugaban gwamnonin Najeriya ya yi magana game da takarar shugaban kasa a 2023

Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, kuma gwamnan jahar Ekiti, John Kayode Fayemi ya warware zare da abawa game da batun tsayawarsa takarar shugabancin kasar nan a zaben shekarar 2023.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito gwamnan ya yi wannan jawabi ne ta bakin mai magana da yawunsa, Segun Dipe, inda ya bayyana cewa ba shi da wani burin tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2023.

KU KARANTA: Gwamnatin jahar Nassarawa za ta kwashe almajirai 63,000 zuwa jahohinsu na asali

Don haka gwamnan yace masu yada wannan jita jita a kansa suna yi ne ba tare da sani ko amincewar sa ba. Mista Dipe ya bayyana cewa duk masu yayata batun basu san Gwamna Fayemi ba, kuma basu san alakarsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar Dipe, duk da cewa Fayemi ya cika dukkanin shika shikan tsayawa takarar shugaban kasa daga yankin kudu maso yammacin Najeriya, amma ya fi son ya cigaba da jan ragamar kungiyar gwamnonin Najeriya tare da kokarin hada kawunan gwamnanonin.

“Manufar Fayemi a matsayinsa na gwamnan jahar Ekiti shi ne ya shiga tsakanin bangarori da basa jituwa da juna, tare da kawo zaman lafiya a tsakaninsu.” Inji shi.

A wani labarin kuma, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana damuwarsa game da bullar annobar cutar Coronavirus a Najeriya da ma duniya gaba daya, do haka ya yi kira ga Musulmai su gudanar da addu’o’I na musamman.

Sultan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar Jama’atil Nasril Islam, JNI, Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya fitar a ranar Laraba, 4 ga watan Maris a garin Kaduna.

Sultan ya yi kira ga Musulmai su dage da tsafta tare da bin duk wasu hanyoyin tsaftace kawunansu don kauce ma yada cutar Coronavirus, sa’annan ya yi kira ga Malamai da limamai su cigaba da wayar da kawunan jama’a akan cutar a dukkanin salloli biyar na kowanne rana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel