Fasto ya bawa mabiyansa maganin bera don ya tabbatar da imaninsu sun sha sun mutu

Fasto ya bawa mabiyansa maganin bera don ya tabbatar da imaninsu sun sha sun mutu

A nahiyar Afrika rashin ilimi ya yiwa mutane katutu da yawa. Mutane da yawa basu ma san menene ya kawo su duniyar ba. Abinda kawai suka sani shine su ci abinci, su kwanta sannan su sadu da iyalansu, a ganinsu wannan shine kawai abinda suke bukata

Haka a wani bangaren akwai mutane da yawa da suke ta faman yaudarar irin wannan mutane da addini. Mutanen da suke zaune a yankunan karkara basu san yanda za su bambance tsakanin mai kyau da marar kyau ba. Suna bin kawai abinda manyan su suka gaya musu.

A 'yan kwanakin nan wani lamari na jahilci da rashin tunani ya faru, inda wani Fasto ya bawa mabiyansa na coci maganin bera suka sha.

Fasto ya bawa mabiyansa maganin bera don ya tabbatar da imaninsu sun sha sun mutu

Fasto ya bawa mabiyansa maganin bera don ya tabbatar da imaninsu sun sha sun mutu
Source: Facebook

Da yawa daga cikin mambobin cocin ta kasar Afrika ta Kudu sun mutu bayan faston ya basu wannan maganin bera sun sha domin su tabbatar da imaninsu ga Allah.

Faston da aka bayyana sunanshi da Priest Light Monyeki daga garin Soshaguve na kasar Afrika ta Kudu, a lokacin da suke gabatar da ibada ya bayyanawa mabiyansa cewa kada suji tsoron mutuwa, saboda baza su mutu ba.

KU KARANTA: Matasa sun yiwa budurwa 'yar madigo fyade domin su gyarata ta fara son maza

Monyeki ya fara zuba musu wani maganin bera a cikin robar ruwa, inda ya bukaci mutanensa da su sha. Bayan Monyeki ya sha kadan daga cikin ruwan robar da ya zuba maganin beran kuma sun ga babu abinda ya same shi, sai suka fara rububin shan wannan maganin bera.

Sai dai yamma nayi da yawa daga cikinsu sun fara karar ciwon ciki, daga baya mutane biyar daga cikinsu suka mutu, aka dauki mutane 13 zuwa asibiti.

Monyeki, yaki yadda ya dauki laifin wannan abu da ya faru ta sanadiyyar sa, a karshe ma sai cewa yayi: "Idan abu mai kyau yayi yawa yana iya zama abu marar kyau."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel