Miyagun yan bindiga sun bude ma jama’a wuta, sun kashe Yansanda 2, wani guda 1

Miyagun yan bindiga sun bude ma jama’a wuta, sun kashe Yansanda 2, wani guda 1

Wasu gungun yan bindiga sun bude ma jama’a wuta a mahadar hanyar Ekete cikin karamar hukumar Udu na jahar Delta, inda suka kashe jami’an Yansanda guda biyu da wani farar hula guda daya.

Jaridar Punch ta ruwaito Yanbindigan sun kai harin ne a daren Talata, 3 ga watan Maris, inda suka kashe yansandan dake tsaron Club 316 ne, sa’annan suka bindige wani farar hula guda daya, tare da kwashe makamansu.

KU KARANTA: Riga kafi ya fi magani: An fara tantance masu ziyarar fadar shugaban kasa don gudun Coronavirus

Duk kokarin da yansandan suka yi na jin ta bakin rundunar Yansandan Najeriya game da lamarin ya ci tura.

A hannu guda kuma, kwamishinan Yansandan jahar Delta, Hafiz Inuwa ya sanar da kama wasu miyagun mutane masu sata tare da garkuwa da jama’an da basu ji ba, basu gani ba a yankin Sapele na jahar.

Kwamishina Inuwa ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Warri inda yace Yansanda sun kama barayin ne a tsakanin ranakun Lahadi da Litinin a Oghara, karamar hukumar Ethiope ta yamma.

A cewar kwamishinan, mutane hudu daga cikinsu sun amsa laifin satar wata mata mai suna Victoria Okereka daga asibitinta a ranar 22 ga watan Feburairu, wanda suka saketa bayan ta kwashe kwana guda a hannunsu.

“Daga ranar Lahadi zuwa Litinin, mun kama wasu miyagu, kuma dukkaninsu suna cikin gungun barayin mutane, an tabbatar da guda hudu daga cikinsu. An gano su, kuma sun amsa laifukansu, amma muna cigaba da binciken sauran mutane biyu.” Inji Inuwa.

Duk dai a jahar Deltan, wani magidanci dan shekara 48 mai suna Felix Edore ya halaka kansa ta hanyar kwankwadar kwalar fiya fiya biyo kama matarsa da ya yi da laifin cin amanarsa ta hanyar neman maza duk kuwa da cewa igiyar aurensu na daure.

Felix ya yanke ma kansa wannan danyen hukunci ne sakamakon bacin rai da ya shiga a sanadiyyar bankado asirin matarsa wanda suka kwashe shekaru 16 suna tare, ashe a bayan idon sa tana neman maza.

Majiyarmu ta ruwaito Felix yana sana’ar tuka motar Tasi ne daga Abraka-Etsu zuwa Sapele a jahar Delta, ya kwankwadi fiya fiya ne a ranar Juma’ar da ta gabata a garin Sapele, inda aka garzaya da shi zuwa asibiti, a washegarin Asabari ya mutu, kamar yadda likitoci suka tabbatar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel