A kowane wata, ina batar da Dala miliyan 2 a kan sadaka - Inji Fasto Mbaka

A kowane wata, ina batar da Dala miliyan 2 a kan sadaka - Inji Fasto Mbaka

Shugaban cibiyar addinin Kiristan nan na Adoration Ministry da ke Garin Enugu, Rabaren Ejike Mbaka ya bayyana adadin kudin da ya ke kashewa ga sadaka.

A Ranar Talata, 3 ga Watan Maris 2020, Ejike Mbaka, ya bayyana cewa duk watan Duniya, ya kan kashe kusan Dala miliyan 2 ga Bayin Allah marasa galihu.

Ejike Mbaka wanda fittacen Fasto ne ya bayyana wannan a lokacin da ya ke gabatar da takardar banki ga wani asibitin da ke Enugu a madadin kungiyarsa.

Faston ya bude kungiya domin tallafawa marasa karfi a karkashin cocin na sa. Sunan wannan kungiya da ya kafa “Multi-Life Savers for the Less Privileged.”

Kamar yadda mu ka samu labari daga wata Jaridar kasar nan, kungiyar ta gabatar da kudi Naira miliyan 18.8 ga wannan asibiti domin a taimakawa marasa lafiya.

KU KARANTA: An sace Malamin kirista bayan ya dawo daga yawon wa’azi

A kowane wata, ina batar da Dala miliyan 2 a kan sadaka - Inji Fasto Mbaka

Fasto Ejike Mbaka ya kan taimakawa jama'a ba tare da an sani ba
Source: Depositphotos

Mbaka ya ke cewa za a kashe Naira miliyan 14 na wannan kudi wajen biyan kudin magani da kudin aikin marasa karfi wadanda ke kwance a asibitin kwararrun.

Jaridar ta ce Faston ya kuma bayyana cewa ya bada kyautar kudi N50, 000 ga ‘Ya ‘yan wata kungiya mai suna Charismatic Renewal of Nigeria da ke Jihar Enugu.

Bayan haka wannan Malamin addinin Kirista ya hadawa ‘Yan wannan kungiya har su mutum 200 kyautar buhun shinkafa domin su samu abin da za su rika kai baki.

“Mu na yin wannan aiki a kowace rana, kuma mu kan ajiye hujja. Babu watan Duniyan da ba na kashe akalla fam Dala miliyan biyu wajen sadaka.” Inji Fasto Mbaka.

Babban Limamin Katolikan ya yi karin haske da cewa: “Saboda haka wannan aikin ya na cikin tarin sadakar da mu ka saba yi ba tare da mun sanar da Duniya ba.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel