Wata sabuwar cuta ta bulla a Jigawa, daruruwan dabbobi sun mutu

Wata sabuwar cuta ta bulla a Jigawa, daruruwan dabbobi sun mutu

Wata sabuwar bakuwar cuta ta bayyana a jahar Jigawa inda ta kashe dabbobi musamman shanu da dama a karamar hukumar Guri ta jahar, kamar yadda jaridar BBC Hausa ta bayyana.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito zuwa yanzu an samu rahotannin mutuwar daruruwan shanu a sakamakon bullar cutar wanda makiyaya suka gaza gane kan ta, amma gwamnatin jahar Jigawa ta musanta zargin da ake yi.

KU KARANTA: Riga kafi ya fi magani: An fara tantance masu ziyarar fadar shugaban kasa don gudun Coronavirus

A cewar kwamishinan ayyukan gona da raya karkara na jahar Jigawa, Muhammad Alhassan, wannan cuta ba bakuwa ba ce, saboda dama can akwai cututtuka irin su Boru da Sammore da kuma ciwon hanya dake samun dabbobi a yankin Margadu, yankin da aka samu mutuwar dabbobin.

Sai dai kwamishinan ya ce jama’a basu fara kai ma gwamnatin koken bullar cutar ba har sai ta fara kassarasu ta hanyar kashe musu dabbobi, bugu da kari yace akwai rahoton mutuwar shanu biyar a karamar hukumar Taura.

A wani labari kuma, fadar shugaban kasar Najeriya ta fara gudanar da tantance ma’aikata da kuma bakin dake ziyartar fadar dake babban birnin tarayya Abuja biyo bayan samun bullar annobar cutar Coronavirus mai suna COVID-19 a Najeriya a ranar juma’ar da ta gabata.

An tura jami’an kiwon lafiya a kofar karshe ta shiga ofisoshin dake cikin fadar shugaban kasa don su tabbatar ma’aikatan fadar gwamnatin tare da baki masu kai ziyara sun wanke hannayensu da ruwan wanke hannu na musamman domin kashe kwayoyin cututtuka dake hannuwan.

Haka zalika jami’an kiwon lafiyan suna amfani da na’urar gwada zafin jikin mutum domin gwajin yanayin zafin ma’aikatan Villa da kuma baki, daga cikin wadanda aka yi ma wannan gwaji a ranar Talata akwai ministan kwadago, Chris Ngige wanda ya isa fadar da misalin larfe 4:50 na rana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel