Nollywood: FFK, Dino, Ezeife sun bayyana a cikin wasan ‘Silent Prejudice’

Nollywood: FFK, Dino, Ezeife sun bayyana a cikin wasan ‘Silent Prejudice’

Mun samu labari cewa Mista Femi Fani-Kayode ya shiga harkar Nollywood, kuma har ya fito a wani shirin wasan kwaikwayo mai suna ‘Silent Prejudice’ da za a saki.

Femi Fani-Kayode ya na cikin Taurarin da su ka fito a kashi na biyu na wannan shiri na ‘Silent Prejudice’. Tsohon Ministan na Najeriya ba bako bane a wajen jama’a.

Fani-Kayode ya fito a cikin wannan wasa ne tare da kyakkaywar tsohuwar matarsa wanda ta yi fice a fagen fim watau Precious Chikwendu, da kuma wasu ‘Yan wasan.

Wannan ne fim na farko da fitaccen ‘Dan siyasar kasar ya yi. Kafinsa an samu ‘Yan siyasa irinsu tsohon Sanata Kogi, Dino Malaye da ya fito a wani wasan kwaikwayo.

Yanzu haka ana karasa kashi na biyu na wannan fim ne a Garin Abuja. A wasan kwaikwayon, an nuna irin kwamacalar da ke cikin sarautar kasar Osu ta Yarbawa.

KU KARANTA: Naziru Sarkin Waka ya mallaki motar da babu irinta a Kannywood

Nollywood: FFK, Dino, Ezeife sun bayyana a cikin wasan ‘Silent Prejudice’
FFK, Dino, Chukwuemeka Ezeife, Ojukwu sun fito a shirin ‘Silent Prejudice’
Asali: Facebook

Ana sa ran cewa fim din zai yi armashi idan ya fito nan gaba domin shugaban hhukumar da ke kula da hakkin Jama’a, Tony Ojukwu, ya na cikin wannan wasan.

Sauran ‘Yan siyasar da su ka shiga cikin fim din sun hada da shi Dino Melaye, tsohon gwamnan jihar Anambra Chukwuemeka Ezeife wanda ya yi mulki a 1992.

Chris Oge Kalu shi ne wanda ya shirya wannan dogon shiri. Taurarin da aka yi amfani da su sun hada da: Clems Ohameze, Amaechi Muonago da Monalisa Chinda.

Sauran wadanda su ka bayyana a fim din da zai fito a Ranar Asabar su ne: Chuks Chyke, Vitalis Ndubuisi, Steve Eboh, Ofiafuluagu Mbaka, da kuma Linc Edochie.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel