Naziru Sarkin waka ya sayi dankareriyar motar da babu wanda ya taba yin irinta a Kannywood

Naziru Sarkin waka ya sayi dankareriyar motar da babu wanda ya taba yin irinta a Kannywood

- Idan ba a manta ba a shekarar da ta gabata, fitaccen jarumi Adam A Zango ya baro wata tsaleliyar mota mai kirar Jeep wacce aka kiyasta kudinta kimanin naira miliyan 27

- A wannan karon kuma fitaccen mawakin nan kuma jarumi, Naziru Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin Wakar San Kano, shi ma ya banbaro motar da babu kamar ta kakaf a masana'antar ta Kannywood

- A shekarar 2018 ma jarumin ya sayo wasu motoci guda biyu masu kirar BMW masu tsadar gaske, sai dai a wancan lokacin ya bayyana cewa gori aka yi masa shine yasa ya sayo motocin

Mawaki Naziru M Ahmad, wanda ake wa lakabi da Sarkin wakar San Kano ya sayo dalleliyar motar da ta dauki hankalin jama’a matuka, aka kuma cika da mamaki musamman jin irin zunzurutun kudin da ya sanya wajen sayen motar.

Sunan sabuwar matar da ya saya AMG G-WAGOON BENZ, sannan mawakin shi ne ya fara dora ta shafin sa na Instagram, inda yayi rubutu kamar haka: “A bude mata.”

Naziru Sarkin waka ya sayi dankareriyar motar da babu wanda ya taba yin irinta a Kannywood
Naziru Sarkin waka ya sayi dankareriyar motar da babu wanda ya taba yin irinta a Kannywood
Source: Facebook

Kamar yadda shafin Kannywood Exclusive suka bincika kuma suka yi kiyasi sun bayyana cewa wannan sabuwar mota ta Nazir Sarkin Waka kudin ta ya ta samma dalar Amurka dubu dari da ashirin da biyar ($125,000), wanda yayi daidai da naira miliyan arba’in da biyar (N45,000,000) a kudin Najeriya.

KU KARANTA: Tashin hankali: Wani mutumi ya yiwa direban mota naushi daya kacal ya mutu

Ko a shekarar 2018 ma dai mawakin ya taba sayo motoci guda biyu kirar BMW wanda kudin su zai iya kai naira miliyan ashirin da biyu. A lokacin ya bayyana cewa gorin motoci aka yi masa, shi yasa ya sayo su.

A ‘yan kwanakin nan dai Adam A Zango ne jarumin da ya sayi motar da ta ja hankalin mutane saboda tsadar ta, inda a shekarar da ta gabata ya sayi motar kirarar Jeep Wrangler da kudin ta ya kai kimanin naira miliyan ashirin da bakwai, hakan yasa ya zama jarumin da yafi kowane jarumi hawa mota mai tsada kafin Nazir Sarkin Waka ya kwace wannan matsayin.

Mawakin dai yayi suna matuka wajen wakokin siyasa dana sarauta a yankin arewacin Najeriya, wannan dalilin ne ma ya sanya Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya bashi sarautar Sarkin Wakan San Kano.

A cikin jaruman dai dama shi da jarumi Adam A Zango ne suke da soyayyar mota, sauran jarumai irinsu Ali Nuhu ba su damu da harkar motoci ba da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel